‘Yan Najeriya na kokawa kan matsalar wutar lantarki

Ana matsalar wutar lantarki a Najeriya

A yayin da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya fara wa`adin mulki karo na biyu, al’ummar kasar na ci gaba da kokawa kan rashin wutar lantarki, wadda hakan ke kara haddasa matsin tattalin arziki.

Duk da kasancewar Najeriya babbar kasa mai arzikin ma’adanin coal da man fetur da iskar gas, sannan kuma wadda ta fi kowacce fitar da danyan fetur a nahiyar Afirka, rahotannin sun nuna kashi 40 cikin 100 na al’ummar kasar ne kadai ke samun wutar lantarki.

Rashin wutar lantarki dai na janyo matsaloli da dama musamman wajen tafiyar da abubuwa da suka hadar da kasuwanci da bangaren aikin gona da masana’antu da asibitoci da makarantu da dai sauransu.

Wani da ke aiki a gamayyar kungiyoyin da ke sa ido kan yadda ake rarraba wutar lantarki a jihar Kano dake arewacin Najeriyar, Malam Nasiru Kura, ya shaida wa BBC cewa, samar da wutar lantarki a Najeriya na tare da matsaloli.

Ya ce tun farko ma ba a bi layin da yakamata abi ba, saboda a Najeriya akwai wasu bangarorin da ke da rana da hamada, to ba a yi amfani da hasken ranar ba wajen samar da wutar.

Malam Nasiru Kura, ya ce dangane da amfani da iskar gas wajen samar hasken lantarkin, har yanzu ana samun jayayya tsakanin kamfanin mai na kasa wato NNPC da kuma NIPP.

Ya ce a yanayin da ake ciki a kasar bisa la’akari da yawan jama’a, to yakamata a ce an samu hanyoyin samar da wutar lantarki da dama, ma’ana a hada da na hasken rana da ta gas da kuma ruwa.

Ya ce, idan har aka yi amfani da wadannan hanyoyin to ko shakka ba bu za a samu wadatacciyar wutar lantarki a kasa, kuma tattalin arzikin kasar ma zai kara habaka.

Karin bayani

Rashin wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya, abu ne da ke ci wa al’ummar kasar tuwo a kwarya musamman wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

Masu sana’oi da dama da ke bukatar wutar lantarkin a koda yaushe na cikin amfani da inji wanda hakan kuma ke sa al’amuransu su rinka komawa baya.

Haka a ma’aikatu ko asibitoci ma, a kodayaushe sai dai kaga ana amfani da inji.

More News

Gwamnan Kebbi ya raba motocin alfarma ga sarakunan jihar

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya miƙa kyautar mota ƙirar Toyota Land Cruiser ga sarakuna huɗu na  jihar masu daraja ta ɗaya. An miƙa muƙullan...

Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan Taraba Darius Ishaku kan naira miliyan 150

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Maitama a Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku kan kuÉ—i naira miliyan 150. A...

Ƴan sanda sun kama mutane 4 da suka sace kayan tallafin ambaliyar ruwa a jihar Borno

Rundunar Æ´an sandan jihar Borno ta ce ta kama mutane huÉ—u da aka samu da sace kayayyakin tallafi da aka bawa mutanen da ambaliyar...

TIRƘASHI: NDLEA ta yi babban kamu a Kaduna

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun kama wasu haramtattun abubuwa da suka kai...