‘Yan kwallon da aka saya a La liga suka kasa taka rawa

Most Expensive La Liga
Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Fiye da Yuro biliyan daya da rabi aka kashe a La Liga kan fara kakar bana wajen sayo ‘yan wasan tamaula.

Kuma kaso 60 daga cikin 100 na cinikayyar da aka yi Real Madrid da Barcelona da kuma Atletico Madrid ne suka fi kashe kudi.

Kungiyoyin uku sun sayo manyan ‘yan kwallo a bana, amma yawancinsu sun kasa taka rawar gani a kakar da muke ciki.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dan wasan da aka saya mafi tsada a Spaniya a bana shi ne Joao Felix, bayan da Atletico ta kashe yuro miliyan 127 wajen dauko shi daga Benfica.

Dan wasan, mai shekara 20, ya fara taka rawar gani daga baya rauni ya kawo masa cikas, tun daga nan ya dunga yin baya a kwazon da yake sawa a fagen taka leda.

Kwallo uku kacal ya ci ya kuma ya bayar da daya aka sa a raga a fafatawa 19 da ya yi wa Atletico.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Antoine Griezmann shi ne na biyu mafi tsada da Barcelona ta saya, bayan da ta biya kunshin kwantiraginsa na yuro fam miliyan 120 daga Atletico.

Dan wasan na tawagar Faransa ya fara nuna kansa zai iya, amma kawo yanzu bai nuna cewar ya maye gurbin Luis Suarez wanda ke jinya ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shi ma dan wasa Eden Hazard da Real Madrid ta sayo daga Chelsea kan yuro miliyan 100, bai yi abin a zo a gani ba a Santiago Bernabeu kamar yadda aka sa ran zai yi.

Jinya ta hana dan wasan tawagar Belgium ya nuna kansa, hasali ma watakila ya kammala buga wasannin kakar bana.

Frenkie de Jong an sa ran da zarar ya fara wasa a Camp Nou kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Sai dai wasu na hangen darajar dan wasan da aka saya yuro miliyan 75 ba ta kai hakan ba, domin ya kasa taka rawar gani kawo yanzu.

Kudin da Real Madrid ta sayo Luka Jovic daga Eintranch Frankfurk wasu na kallon an caka mata shi ne.

Dan wasan bai buga tamaula sosai karkashin koci Zinedine Zidane a bana, kuma kamar dai haka zai ci gaba da zaman benci har a karkare wasannin shekarar nan.

Haka ma Eder Militao bai nuna zai iya gadar Sergio Ramos ko ya karbe gurbin Raphael Varane a matsayin mai tsaron baya ba.

Kuma kimanin yuro miliyan 50 Real ta biya Porto, kodayake wasu suna cewa Jovic da Militao matasa ne sai nan gaba za a ga amfaninsu.

Ferland Mendy daya ne daga cikin ‘yan kwallon Real Madrid da ta sayo da tsada, shi dai ya nuna kansa, inda dan wasan mai shekara 24 kan ajiye Marcelo a benci.

Ya kuma koma Santiago Bernabeu kan yuro miliyan 48 daga Lyon ta Faransa.

Shi ma Rodrygo, yana taka rawar gani domin yana cin kwallo yana kuma taimakawa ana zura su a raga, tun bayan da ya koma Spaniya da taka leda kan fam miliyan 45 daga Santos.

‘Yan wasa biyu masu tsada daga cikin 10 da aka saya a Spaniya masu taka leda ne a Valencia.

Jasper Cillessen ya koma Valencia daga Barcelona kan yuro miliyan 35, sai dai yana ta fama da jinya, inda har yanzu kungiyar na jiran kwazon da zai yi mata nan gaba.

Haka ma Valencia na jiran rawar da Maxi Gomez zai taka, bayan da ya koma kungiyar kan yuro miliyan 34.5 daga Celta Vigo.

Cikin wadanda aka saya a watan Janairu kuwa kamar Raul de Tomas da Youssef En-Nesyri da kuma Paco Alcacer, an hakikance cewar za a iya sayen zakakurin dan wasa duk da kakar tamaula ta yi nisa.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...