Yan kasar China uku sun gurfana a kotu kan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wasu yan kasar China uku a gaban wata babbar kotun tarayya dake birnin Abuja inda ake zargin su da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Hukumar tsaron Civil Defense ce ta gurfanar da mutanen a gaban kotun a madadin gwamnatin tarayya.

Mutanen da ake zargi da kuma kamfanin su Lian Hua Quarry Nigeria Limited ana musu tuhume-tuhume uku da suka haÉ—a da haÉ—a baki da kuma haÆ™ar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Lauya mai gabatar da aka Æ™ara, Alex Ojo ya bukaci a tsare waÉ—anda ake zargi a gidan yari har zuwa lokacin da za a fara sauraron shari’ar.

More News

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuÉ—aÉ—e

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...