‘Yan gudun hijira za su samu tallafin dala miliyan 4.6

EPA

Hakkin mallakar hoto
EPA

—BBC Hausa

Majalisar wakilai a Amurka ta amince da wani kudurin doka inda za a samar da dala miliyan hudu da dubu dari shida domin tallafawa masu fama da matsi da kuma fatara da ke kan iyakar kasar.

Tuni dama ‘yan majalisar dattawan kasar suka amince da kudirin dokar inda kuma a yanzu ana jiran shugaban Amurkar Donald Trump ya rattaba mata hannu domin ta fara aiki.

An dai amince da dokar ne bayan da ‘yan jam’iyyar Democrats hakar su ta gaza cimma ruwa ta bangaren kara daukar matakai domin kare ‘ya’yan baki da suke gudun hijira kasar.

Shugabar Majalisar Wakilan Kasar Nancy Pelosi, ta bayyana cewa samar da kudade domin tallafa wa a kan iyakar kasar shi ne babban abin da yakamata a yi.

Ko a kwanakin baya dai Fafaroma Francis ya bayar da tallafin dalar Amurka dubu 500 ga ‘yan gudun hijira.

An bayyana cewa kudin za su amfani ‘yan gudun hijiran da suke gararamba ko kuma suka rasa mafaka a Mexico a kokarin da suke yi na tsallake iyakar Amurka.

Hakazalika ko a kwanakin baya hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yawan mutanen da tashin hankali ya raba da muhallansu ya wuce miliyan 70, adadi mafi girma da aka taba gani a tarihi.

A kididdigar da hukumar ke fitarwa duk shekara, ya nuna mutanen da yaki ke tilastawa barin gida, na gagara samun wurin da za su zauna cikin kwanciyar hankali.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...