‘Yan gudun hijira 33, motoci 15, buhunan Shinkafa sun fada hannun hukumar Kwastam

Jami’an hukumar Kwastam na Najeriya masu maganin fasa kauri sun cafke wasu mutane 33 da su ka yi kokarin shigowa cikin kasar a boye. Kakakin hukumar ya sanar da wannan a makon nan.

A Ranar Talata, 27 ga Watan Agusta, 2019, Mai magana da yawun bakin hukumar ta Kwastam, Joseph Attah, ya bayyana cewa su na samun nasara a shirin nan na “Exercise Swift Response.”

Mai magana a madadin hukumar, ya ce hakar wannan aiki ta na cin ma ruwa domin sun kama masu shigowa Najeriya babu takardu, sannan kuma sun tare wasu motoci da kayan fasa kauri.

Motoci 33 da aka shigo da su Najeriya ta barauniyar hanya su ka kare a hannun jami’an na NCS. Daga cikin kayan da aka samu har da buhuna 3560 na shinkafar kasar waje masu nauyin kilo 50

Bayan haka kuma jami’an kasar sun cafke wasu buhuna takin zamani na NPK 59 da aka nemi a shigo da su a boye. A jawabin da Attah ya fitar jiya, ya ce sun kuma kama masu shigo da mai.

Gangar man gyada 65 jami’an na Kwastam su ka karbe a wajen wannan aiki da a ke yi na “Exercise Swift Response.”

Ma’aikatan sun kuma dakile manyan ganguna 12 dauke da fetur.

Ofishin NSA mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Najeriya ne ya kawo wannan aiki na “Exercise Swift Response.” Kwastam ta na aiki ne da sauran hukumomi irinsu ‘yan sanda.

Yanzu dai an fara ganin tasirin wannan aiki na hadaka da a ke yi da jagorancin kwastam da NIS masu kula da shiga da fice da kuma Dakarun sojin sama da sauran jami’ai a yankunan kasar

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...