‘Yan fashin daji sun sake auka wa Ć™auyukan Zamfara da Sokoto

Jihar Zamfara

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan fashin daji sun kashe sama da mutum 30 lokacin da suka auka wa kauyen Dan-Gurgu a farkon watan Mayu

ĆŠumbin mutane ne rahotanni suka ce sun tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji a yankunan Isan jihar Sokoto da ma na Zamfara mai maĆ™wabtaka tun daga farkon wannan mako.

Bayanai daga ƙaramar hukumar Shinkafi sun ce gomman mutane ne suka fantsama manyan garuruwan yankin kamar ita Shinkafin don kuɓuta da rayukansu.

Wata shaida da ta tsere daga ƙauyen Kamarawa ta faɗa wa BBC daga inda ta fake a cikin daji cewa sun baro gidajensu ne lokacin da suka ga mahara na far wa mazajensu tare da yin awon gaba da dabbobi.

“A jiya (Litinin) da safe, sai muka ga jiragen sama suna ta yawo a yankinmu, sai suka sauka jejin da É“arayin suke, suna ta sako musu bom-bom da bindigogi. Ga sojoji daga sama suna ta yin shuuu,” in ji matar.

Ta ce sun yi ta murna don kuwa suna tunanin wahala ta yanke musu. “Muna cewa Ć™ila za a É—auke mana mutanen nan ne.”

Sai dai ta ce lafawar da aka samu ta jami’an tsaron sai ‘yan fashin dajin da suka noĆ™e suka sake far wa Ć™auyukan yankin. Ta ce daren jiya (Litinin) Ć™auye uku suka tayar.

“Ka ga asibitin Shinkafi, akwai mutane kwakkwance, asibitin Isa, akwai mutane kwakkwance. Yanzu kuma yau (Talata) Kamarawa, tun da mangariba suka shiga, sun gewaye ta gaba É—aya,” in ji shaidar.

Maharan dai sun kai hare-haren ne a kan babura inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.

Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da mutanen ƙauyen Danfasa cikin ƙaramar hukumar Maru a Zamfara ke juyayin sace mata 20 da kuma mutum bakwai da aka kashe a wani hari da yammacin ranar Litinin.

Wani mutumin ƙauyen ya faɗa yayin zantawa ta wayar tarho cewa suna tsakiyar cin kasuwa a wani ƙauye mai maƙwabtaka da su ne ranar Litinin lokacin da maharan suka far wa gidajensu a Danfasa da yamma.

A cewarsa, baya ga mutanen da aka jikkata, an kuma kashe mace biyu da namiji biyar cikinsu har da dattijai guda biyu.

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Army

Image caption

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta lalata sansanonin ‘yan fashin daji da dama

Shaidan wanda ya ce an ƙone kusan rabin ƙauyensu, ya ce a halin da yake magana ma yana kan hanyarsa ne ta barin yankin saboda rashin tabbas a garuruwansu.

Ya ce daga ciikin mata ashirin da ‘yan fashin suka sace har da ‘yarsa mai kimanin shekara talatin, ya kuma ce har yanzu ba su ji amo ko labarinsu matan ba.

Mutumin ƙauyen Ɗanfasa ya kuma koka kan rashin kai musu ɗauki don kuɓutar da iyalinsu da dukiyarsu daga maharan, duk da neman gudunmawar da suka yi a wajen hukumomi.

Jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina dai sun daÉ—e suna fama da hare-haren ‘yan fashin daji, duk da matakan da gwamnatin Najeriya kan ce tana É—auka don kawo Ć™arshensu.

A baya-bayan nan ma sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa al’ummar jihar Katsina haĆ™uri tare da cin alwashin É—aukar Ć™waƙƙwaran mataki don murĆ™ushe ‘yan fashin da suka addabi sassan yanki.

Zuwa yanzu dai jami’an tsaron Najeriya ba su tabbatar ko musanta rahotannin kai wadannan hare-hare ba.

Kuma ga alama sai nan gaba ne za a iya tantance irin ɓarnar da maharan suka haddasa a ƙauyukan da suka far wa musamman na baya-bayan nan garin Kamarawa.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...