Yan fashin daji sun kashe jami’ai biyu na hukumar lura da shige da fice ta Najeriya a jihar Kebbi

Hukumar Lura Da Shige da Fice Ta Najeriya ta ce ta jami’anta biyu sun mutu a wani harin da yan fashin daji suka kai jihar Kebbi.

Mai magana da yawun hukumar a jihar Kebbi, DSI Abdullahi Isa shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Laraba da aka fitar Birnin Kebbi.

Ya ce a ranar Litinin ne 15 ga watan Janairu wasu da ake zargin yan fashin daji ne suka kai hari kan shingen bincike na jami’an dake ma shigar shigowa Najeriya ta Garin Garba mai tazarar kilomita 12 daga garin Kangiwa hedkwatar karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.

Sanadiyar haka ne jami’an biyu Isa Nafiu da Garba Haruna Fana suka rigamu gidan gaskiya a cewar mai magana da yawun hukumar.

Ya kara da cewa daya daga cikin jami’an ya tsira da ransa a harin.

Tuni dai aka yi jana’izar ma’aikatan biyu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a birnin Kebbi.

More from this stream

Recomended