‘Yan fashi sun halaka sama da mutum 30 a Zamfara – Basaraken Dan Sadau

Jihar Zamfara

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sarkin Kudun Dan Sadau a jihar Zamfara ya tabbatar wa BBC cewa ‘yan fashin daji sun kashe sama da mutum 30 lokacin da suka auka wa kauyen Dan-Gurgu na masarautarsa tare da jikkata karin wasu 12.

Alhaji Hussaini Umar ya ce dukkan mutanen da abin shafa maza ne, wadanda aka far wa a lokacin da suke haramar tafiya gonakinsu wayewar garin ranar Asabar.

BBC ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammed Shehu kan wannan rahoto, sai dai bai amsa kiran waya da muka yi ta yi masa, ko musanta gajeren sakon da muka aika masa ba.

Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na fama da hare-haren ‘yan fashin daji, wadanda kan far wa kauyuka, su kashe mutane, tare da kona gidajensu har ma da dukiyar da suka mallaka. Ko da yake da farko sun fara ne da satar mutane, inda sukan rike su har sai dangi ko makusantansu sun biya kudin fansa.

Masarautar Dan Sadau da ke karamar hukumar Maru ta yi makwabtaka da yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, wanda ya yi kaurin suna wajen hare-haren ‘yan fashi da satar mutane.

Maharan a kan babura kimanin saba’in sun rika harbi kan mai uwa da wabi, Alhaji Hussaini Umar ya ce shi da kansa ya je asibitin Dan Sadau inda ya jajantawa mutanen da aka jikkata su goma sha biyu.

A cewar basaraken: “Likitan da ke kula da mutanen da aka jikkata ya tura biyu daga cikinsu zuwa babban asibiti saboda raunukan da aka ji musu sun tsananta.”

Ya koka game da karancin kayan aikin da jami’an tsaron da ke yankin masarautar Dan Sadau, inda ya ce: “Na yi magana da DPO lokacin da aka bugo (waya) aka hwada mana ga abin ke hwaruwa, amma al-hakikanin gaskiya, matsala bai da abin hawa kuma bai da yara mataimaka wadatattu wadanda za su iya yin hanzari (kai dauki) ga lokacin da wani abu ya hwaru.”

Alhaji Hussaini ya ce tuni mazauna kauyen Dan Gurgu suka fara tsere wa gidajensu zuwa makwabtan garuruwa da suke ganin sun fiye musu aminci.

Basaraken ya yi kira ga gwamnati da ta kai musu agaji don kuwa a cewarsa: “har yanzu mutanena suna cikin halin kaka-ni-ka-yi, manoma ba su iya zuwa don tunanin sassaben gonakinsu da shirye-shiryen gyaran ayyukan gona.”

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...