‘Yan ci-rani 170 ne Suka halaka a tekun Bahar Rum – MDD

0
More than 4,200 migrants reportedly crossed to Europe in the first 16 days of 2019

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Kimanin ‘yan ci-rani 4,200 ne suka tsallaka teku zuwa Turai a kwanaki 16 na shekarar 2019 kawai

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa mutum 170 ne suka mutu a wasu hatsarin jirgin ruwa biyu da suka auku a tekun Bahar Rum.

A wata sanarwa da shalkwatar hukumar ta fitar a birnin Geneva, ta ce labarin mutuwar mutanen ya gigita ta, kuma ta yi kira ga kasashen Turai da su tashi tsaye wajen samar wa ‘yan gudun hijira hanyoyi masu sauki na shiga nahiyar Turai.

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce wani jirgi da ya dauko ‘yan gudun hijira da ‘yan ci-rani akalla 50 ya nutse a yammacin tekun Bahar Rum tsakanin Maroko da kasar Spaniya.

Mutum daya ne kawai ya tsira da ransa, wanda shi ma wani jirgin masunta ne ya tsinto shi.

Wannan hatsarin ya biyo bayan wani irinsa da ya auku, inda sojojin ruwa na kasar Italiya na can na neman wasu mutum 117 da ba a san inda suka shiga ba, kuma mutum uku kawai aka gano kawo yanzu.

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta ce ba za ta iya tabbatar da yawan wadanda suka mutu ba, amma ya zama wajibi a kawo karshen wannan asarar rayukan da ake yi.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Wani dan gudun hijira da aka ceto daga tekun Bahar Rum

Hukumar ta damu da matakan da wasu kasashen Turai ke dauka na hana kungiyoyin sa kai ceto irin mutanen da suka sami kansu a irin wannan mawuyacin halin.

A karshe hukumar na so a fitar da wani sahihin tsarin da zai hana ‘yan gudun hijira shiga hannun masu fasa kwaurin mutane domin shigar da su Turai ta barauniyar hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here