‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan kamfanin Shell su biyu

Wasu ma’aikatan kamfanin mai na Shell su biyu sun fada hannun masu garkuwa da mutane a jihar Rivers.

Har ila yau masu garkuwar sun kashe jami’an ƴansanda biyu dake yiwa ma’aikatan rakiya.

Lamarin yafaru ne a kan titin East West dake a jihar ta Rivers.

Manya ma’aikatan biyu ana kama sun e lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga jihar Bayelsa bayan wata ziyarar aikin da suka kai.

More from this stream

Recomended