Yan bindiga sun yi garkuwa da DPO a Nasarawa

CSP Haruna Abdulmalik DPO na yan sanda dake karamar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa ya fada hannun masu garkuwa da mutane.

Babban jami’in ɗan sandan na gudanar da aikin sintiri da daddare akan hanyar Nasarawa-Eggon zuwa Akwanga lokacin da yayi kacibus da yan bindigar da suka rika harbin iska ba kaƙƙautawa kafin su yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba

An ce DPO ya samu bayanin yadda ƴan bindiga suke addabar yankin Nassarawa Eggon a yayin da ya ke kokarin shawo kan lamarin sai aka sace shi.

Wasu mutane dake yankin sun bayyana damuwarsu kan faruwar lamarin inda suka ce tun bayan da aka tura shi yankin yake ta ƙoƙarin ganin ya raba su da yan ta’addan da suka addabesu.

More News

Kar ku ɓata rayuwarku da shan miyagun ƙwayoyi, Aisha Buhari ta faɗa wa yara

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, a ranar Asabar, a Abuja, ta bukaci yara su kasance masu kishin kasa ta hanyar "kaucewa" shan kwayoyi. "Muna son...

Mun ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu—Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin ranar hutu a fadin kasar nan a hukumance. Matakin dai...

Buhari ya zagaya da Tinubu a cikin Villa

Yadda Shugaban Najeriya bai barin gado, Muhammadu Buhari, ya zagaya da Shugaba mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, a cikin fadar shugaban kasa. Ranar Litinin...

Hoto:Kwankwaso Ya kaddamar da wasu ayyuka a Kaduna

Biyo bayan gayyatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi masa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar da wasu...