Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Daliban Makaranta A Jihar Kaduna


Ya zuwa lokacin hada wannan labari ba’a iya tantance adadin daliban da ‘yan bindigan suka sace ba.
T o sai dai wata Majiya daga bakin kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa, a halin yanzu shi da wasu jami’an gwamnati suna cikin makarantar kuma suna bincike don gano adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace.
Wata É—alibar makarantar da ta bukaci a sakaya sunan ta, ta shaida cewa a cikin dare ne maharan suka far wa makarantar tana mai cewa an tafi da kusan rabin dalibai mata na makarantar, haka kuma ba’a tafi da dalibi namiji ko É—aya ba.
Ya zuwa wannan lokacin dai, gwamnati jihar Kaduna ko jami’an tsaro ba su tabbatar da afkuwar wannan lamarin ba a hukumance.
Wani ganau dake da ke zama a unguwar Mando a jihar Kaduna ya bayyana cewa da misalin karfe 11 da rabi na dare sun rika jin harbi amma sun yi zaton a Makaratar Horar da Sojoji ta NDA ne.
” Akwai lokuta da dama a yayin bada horo a NDA su kan yi harbi cikin dare tunda makarantar sojoji ce”, in ji mazauni unguwar, ya kara da cewa da asuba da suka fita sallah ne suka sami labarin abin da ya faru.
Majoyoyi daga unguwar Kawo dai sun bayyana cewa, jami’an tsaro sun kewaye makarantar kuma an kwashe ragowar daliban da ba’a sace ba aka tafi da su makarantar NDA.
Batun sace daliban makaranta da ‘yan bindiga ke yi a baya-bayan nan na kara kamari, wanda a watan jiya ma sai da suka sace matafiya, da dalibai makarantun sakandare na gwamnati a Kagara da ke jihar Neja, da ta Jangebe a jihar Zamfara.

More News

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...