Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland.
A ranar 22 ga watan Afrilu ne shugaban ƙasar ya bar birnin tarayya Abuja ya zuwa ƙasar Nezaland inda ya kai ziyarar aiki.
A lokacin mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya ce Tinubu ya kai ziyarar ne biyo bayan gayyatar da firaministan ƙasar , Mark Rutte ya yi masa.
Bayan kammala ziyarar ta Nezaland shugaban ƙasar ya wuce ƙasar Saudiya inda ya halarci taron tattalin arziki duniya da aka gudanar a ranakun 28 da 29 ga watan Afrilu.
Tun bayan halartar taron ne ba a ƙara jin ɗuriyar shugaban kasar ba inda wata majiya dake kusa da shugaban ta bayyana cewa ya wuce birnin Paris na ƙasar Faransa a wata ziyara ta ƙashin kansa.
Hakan ya sa wasu ƴan adawa ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar suka fara kiraye-kirayen da a bayyana inda shugaban ƙasar ya ke.