Yan bindiga sun kashe yan arewa 6 a Ondo

Wasu yan bindiga da tsakar daren ranar Talata sun kashe wasu mutane 6 yan arewacin kasarnan a yankin sabo dake Akure babban birnin jihar Ondo.

Tuni aka yi jana’izar mutanen ranar Laraba yayin da daya daga cikinsu ke cigaba da karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Harin na zuwa ne yayin da jihar ke cigaba da jimamin mutuwar mutane kusan 40 da wasu yan bindiga suka harbe a cocin Katolika ta San Francis dake garin Owo na jihar.

Sarkin Hausawan Ondo, Alhaji Abdulsalam Yusuf ya ce yan bindigar akan babur sun dira akan babur inda suka bude wuta kan mutanen.

“Sun zo yankinmu na Sabo akan babura kowanne dauke da yan bindiga uku kwatsam sai suka fara bude wuta kan mutane, yawancin su masu shayi da suya. ” Ya ce

Yusuf ya ce harin kamar na ramuwar gayya ne kan kisan mutanen da aka yi a cocin domin su sun dade suna zaune a yankin lafiya ba tare da tashin hankali ba.

More from this stream

Recomended