‘Yan bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Jihar Kebbi

Haren-haren ta’addanci na ci gaba da zama sanadiyar rashin rayuka da dukiyoyin jama’a a Najeriya musamman a arewacin kasar. 

A Najeriya duk da ayyana ‘yan fashin daji da gwamnatin kasar tayi a zaman ‘yan ta’adda har yanzu ana samun rahotannin hare-hare da suke kaiwa tare da kisa ko yin garkuwa da jama’a.

‘Yan bindiga sun kai wani hari a yankin kudancin jihar Kebbi inda kawo yanzu ba’a san adadin mutanen da suka hallaka ba, duk da yake suma an kashe wasu daga cikin su.

Haren-haren ta’addanci na ci gaba da zama sanadiyar rashin rayuka da dukiyoyin jama’a a Najeriya musamman a arewacin kasar.

Mahara sun kai hari a wani gari mai suna Dan Kade dake yankin Unashi a masaurautar Zuru ta jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya yankin da ya sha fama da harin ta’addanci a can baya.

Yanzu haka akasarin mazauna kauyen wadanda harin bai kai wurin su ba sun kauracewa garin domin maharan suna kona gidajen jama’a.

Wani mazaunin garin Bello Dan Kade ya ce a halin yanzu ba su san iyakan gawarwakin da aka kashe aka kona ba.

Muryar Amurka ta tuntubi rundunar ‘yan sandan Najeriya akan batun amma kakakin rundunar a Kebbi bai dauki kiran nasa ba.

Shi ma mashawarcin gwamnan Kebbi kan tsaro bai amsa kiran da na masa ba.

Ko da shi ke shugaban kungiyar tsaro ta ‘yan sakai na masaurautar Zuru Mani John ya kara tabbatar da harin da aka kai.

Duba da ganin mahara har yanzu suna addabar jama’a ya sa masana lamurran tsaro ke ganin ya kamata gwamnati ta sauya yadda take yaki da maharan da yake a hukumance an ayyana su a zaman ‘yan ta’adda a cewar shugaban sashen nazarin lamurran laifuka da tsaro da jama’ar Yusuf Maitama Sule, detective Auwal Bala, Durumin iya.

Mazauna yankunan da ke da matsalolin rashin tsaro na kyautata fatar gwamnati za ta kara azama da yake tana kan fafatawa da ‘yan ta’addar domin tsaron rayukan ‘yan kasa.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...