Yan bindiga sun kai hari kan ofishin yan sanda a Kogi

Da tsakar daren ranar Juma’a ƴan bindiga suka kai hari kan ofishin shiya na yan sanda dake Eika Ohizenyi a karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi inda suka kashe wani Insifecta Jibril dake bakin aiki.

Wani mazaunin yankin, Mallam Momoh Abubakar ya bayyana cewa maharan sun mamaye ofishin yan sandan da misalin 12:15 na tsakar daren ranar Juma’a dauke da bama-bamai da sauran makamai.

Ya bayyana cewa bom na farko da suka jefa kan ofishin ya yi karar gaske da ta tashi mutane da dama daga bacci a yankin ya kara da cewa bama-baman sun lalata wani sashe na ginin ofishin.

Abubakar ya kara da cewa maharan sun ci karensu babu babbaka inda suka shafe sama da sa’o’i biyu ba tare da wani ɗauki ba daga jami’an tsaro ko kuma mutanen gari.

Ya bayyana cewa jami’in dan sanda ɗaya tilo dake bakin aiki, Jibril wanda aka fi sani da Yellow an kashe shi a harin yayin da aka lalata motar sintiri ɗaya da ofishin yake da ita.

Yan bindigar sun lalata tagogin babban masallacin Eika da kuma na cocin Katolika dake garin.

Tuni kwamishinan yan sandan jihar, Edward Egbuka ya bada umarnin tura karin jami’an tsaro zuwa yankin.

More News

Kar ku ɓata rayuwarku da shan miyagun ƙwayoyi, Aisha Buhari ta faɗa wa yara

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, a ranar Asabar, a Abuja, ta bukaci yara su kasance masu kishin kasa ta hanyar "kaucewa" shan kwayoyi. "Muna son...

Mun ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu—Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin ranar hutu a fadin kasar nan a hukumance. Matakin dai...

Buhari ya zagaya da Tinubu a cikin Villa

Yadda Shugaban Najeriya bai barin gado, Muhammadu Buhari, ya zagaya da Shugaba mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, a cikin fadar shugaban kasa. Ranar Litinin...

Hoto:Kwankwaso Ya kaddamar da wasu ayyuka a Kaduna

Biyo bayan gayyatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi masa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar da wasu...