
Yan bindiga sun buɗe wuta kan ayarin motacin alhazai a ranar Litinin a Sokoto.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da ake kai maniyyatan filin jirgi domin su tashi zuwa kasa mai tsarki a ranar Talata.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa wasu daga cikin ƴan bindigar sun samu raunuka lokacin da suke musayar wuta da jami’an tsaron da ake bawa ayarin motocin kariya.
Yan bindigar sun yi wa mahajjatan kwanton bauna a wajen dajin Gundumi amma jami’an tsaro sun samu nasarar dakile hari.
Babban sakataren din-din a hukumar alhazai ta jihar Sokoto,Shehu Dange ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Muna san mu san halin da maniyyatan suke ciki. An ceto su duka? Ko kuma akwai wani daga cikin su da ya jikkata,” ya ce.