‘Yan bindiga sun afka wa kauye a Jigawa

Barayi yan bindiga dake kan babura sun farma kauyen Abaya dake kan hanyar Wurma a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa.

Barayin da suka farma kauyen ranar Laraba da daddare ana zargin sun harbe kusan mutane sama da 30.

Har ya zuwa lokacin da jaridar Daily Trust ta wallafa labarin babu cikakken bayanai kan adadin mutanen da abin ya rutsa da su.

Amma wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kashe wasu mazauna kauyen yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon raunin harbin bindiga.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...