‘Yan bindiga na barazanar kisa ga ma’aikatan lafiya

Wani ma'akacin lafiya kenan a lokacin da ya ke dauke da wani jariri dan kwana 4 wanda ake zargin cewa yana dauke da Ebola, kafin a shiga da shi cikin wani wurin kullawa da masu cutar a Butembo da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A cikin shekarar da ta gabata kusan mutum 1800 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

“Mutane suna tunanin cewa babu gaskiya a batun yaduwar cutar Ebola,” a cewar Dokta Pascal Vahwere, wani likita da ke kokarin dakile cutar. “Tawagata na fuskantar barazana domin aikin da muke yi”.

Dakta Vahwere ya shaida wa BBC cewa a cikin watan Maris da ya gabata, wasu gungun mutane sun kai masa hari a lokacin da yake jagorantar wata kungiya ta ma’aikatan lafiya domin zuwa wani kauye domin bayar da rigakafin cutar a yankin arewacin Kivu na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

“Kwatsam sai wani gungun mutane masu dauke da bindiga suka afka mana. Ba mu san dalilinsu na kawo mana hari ba. Mun tsorata. Daga baya mun yi magana da shugabanin yankin, lamarin da ya jawo mutanen suka watse.”

Ma’aikatan lafiya na neman wadanda suka kamu da cutar, sai su kawo su cibiyoyin da aka ware domin kulawa da su. Suna kuma taimakawa wajen binne wadanda suka mutu.

Sai dai abu ne mai hadarin gaske ga ma’aikatan lafiyar su shiga wuraren da ake fama da cutar.

Hakkin mallakar hoto
MSF

Image caption

Masu dauke da bindiga sun kai hari kan wata cibiyar kulawa da Ebola da ke Butembo, a gabashin Kongo. Lamarin dai ya janyo mutuwar dan sanda daya da kuma raunata wani ma’aikacin lafiya.

A yayin da cutar take ci gaba da yaduwa, tana kuma kara halaka mutane kuma ma’aikatan lafiya na fuskantar fushin masu dauke da makamai sakamakon zarge-zargen da ake yadawa musamman a dandalin Whatsapp.

Akalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a cikin shekarar nan kawai. BBC ta yi magana da masu yaki da cutar kan dalilin da ya sa hakan ke faruwa.

Zarge-zarge

Zarge-zarge da kuma rashin daukar cikakkun matakai kan cutar ne ke haifar da kiyayya tsakanin mutanen da za su iya kamuwa da cutar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

At least seven health workers have been killed this year in DRC

“Yaduwar labaran bogi ya jawo mutane sun yarda cewa Ebola hanya ce ta samun kudi ga ‘yan siyasa,” a cewar Dr Vahwere.

Yana aiki ne da wani kwamitin ceto mutane na kasa da kasa da ke birnin Goma wanda ke gabashin DRC.

Birnin ya bayyana cewa mako biyu da suka gabata ne ya fara rasa mutum daya sakamakon cutar, inda a farkon makon nan kuma aka samu mutum daya da ya kamu da cutar.

“Wasu har cewa suke yi maganin Ebolan ne ke kashe mutane,” in ji shi.

Hare-Hare

An samu karuwar hare-hare kan ma’aikatan lafiya tun bayan da aka fara yada zarge-zargen.

“Tun 1 ga watan Janairun 2019, an kai hari 198 kan cibiyoyin lafiya da kuma ma’aikata da ke karkashin hukumar kula da lafiya ta duniya WHO.

“Lamarin ya jawo mutuwar mutum 7 da kuma 58 da suka samu raunuka a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo,” kamr yadda Sakuya Oka wani manajan sadarwa na WHO ya shaida wa BBC.

Hakkin mallakar hoto
Institute of Tropical Medicine

Image caption

An kashe Richard Mouzoko a yayin wani harin da aka kai kan asibitin jami’ar Butembo

A cikin wadanda suka rasa rayyukansu har da wani babban mai bincike kan cutuka na WHO, Richard Mouzoko.

An kashe shi ne a yayin wani harin da aka kai kan asibitin jami’ar Butembo a ranar 19 ga watan Afrilu. Mutum biyu ne suka samu raunuka a yayin harin.

A cikin watan Mayu mazaunan wani kauye da ke gabashin Kongo sun kashe wani ma’aikacin lafiya tare da kuma sace abubuwan da ke cikin cibiyar ta kula da lafiya.

A ranar 15 ga watan Yuli an kashe wasu ma’aikatan lafiya masu yunkurin dakile Ebola a gidajensu da ke yankin Kivu na arewacin kasar.

Yaduwa

Yadda ake samun karuwar hare-hare na rage kaifin yadda hukumomi ke tunkarar cutar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gwamnatin Kongo ta aika wasu jami’an tsaro domin su kare ma’aikatan lafiyar

Cutar na ci gaba da yaduwa cikin gaggawa – a cikin kwannaki 224 ne dai mutum 1000 suka kamu da cutar, cikin kwanaki 71 kuma wasu 2000 suka sake kamuwa.

“A yau mun samu nasarar dakile cutar daga kan mutum 57 a cikin wata cibiyar kula da cutar ta Beni. Hakan na nufin kenan muna aikin mu da kyau,” a cewar Dakta Freddy Sangala.

Ebola cuta ce wadda ke yaduwa ta ruwan jikin mutum kamar ruwa da kuma kayayyaki ko barguna wadanda wannan ruwan ya taba. Babu maganin Ebola, amma shan magani idan aka yi hasashen cewa mutum na dauke da ita zai iya taimakawa wajen samun nasarar dakile ta.

Rigakafi

An kirkiri wani sabon rigakafi wanda ake bai wa mutane a DRC domin taimakawa wajen dakile yaduwar cutar ta Ebola.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Riga kafin da ake yi na fuskantar cikas saboda yawan hare-haren da ake kai wa kan ma’aikatan lafiyan

An yi wa kusan mutum 170,000 wadanda suke da alaka da masu dauke da cutar rigakafi.

Amma hare-haren na kawo cikas kan shirin na yi wa mutane riga kafi, wanda hakan ke baiwa cutar karin damar yaduwa.

Rashin yarda da kuma mayaka

Yaduwar Ebola na faruwa ne a yankin da ke da a kalla kungiyoyin ‘yan tawaye 24. A cikinsu har da wadanda gwamnati ke zargin cewa sun kai hare-hare kan ma’aikatan lafiya.

Babban darakta janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya wallafa wani sako a ranar 10 ga watan Mayu bayan da ma’aikatan lafiya suka fuskanci hare-hare cewa:

”Abin tausayin shi ne ba mu da yadda za mu yi mu dakile Ebola, amma idan aka ci gaba da kai hare-hare to dakile yaduwar zai fi zama abu mai wuya.”

A arewacin Kivu, wata kungiyar masu dauke da bindiga wadanda ake kira “Mai-Mai” ne ke da hannu a wasu hare-hare kan ma’aikatan lafiyar da kuma cibiyoyinsu, a cewar gwamnati.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sakamakon wasu hare-haren da ake kaiwa, wasu ma’aikatan lafiya na fargabar a gan su da kayayakin aikinsu

An zargi wata kungiyar masu bindiga mai suna Allied Defence Forces wato ‘yan tawayen Uganda kenan masu aiki cikin Kongo da lalata wasu cibiyoyin lafiya.

An kuma samu hare-hare daga wasu kungiyoyi da ba a san ko su wane ne ba kan cibiyoyin da ake kula da masu Ebola.

An taba samun wani lamari a watan Mayu, inda wasu ‘yan uwa suka ci zarafin wasu ma’aikatan lafiya wadanda ke binne daya daga cikin ‘yan uwansu.

Kariya daga soji

Karuwar hare-haren dai ya jawo abubuwa da dama.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An aika sojoji zuwa wasu yankuna domin kare ma’aikatan lafiya da kuma cibiyoyinsu

“Bayan kowane hari dai, ana samun karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar,” a cewar Amy Daffe.

Domin kare ma’aikatan lafiyar, gwamnati na kara aika jami’an tsaro domin tsare su.

Cutar kyanda

Kate White wata nas ce kuma tana aiki da kungiyar da ke bayar da tallafi a fannin lafiya ta kasa da kasa, mai suna Doctors without Borders.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yanzu ana tantance mutane kafin su iya shigowa Goma

Ta shaida wa BBC dalilin da ya sa ba a cika yarda da juna a yankin ba.

”Al’ummomin na fama da rashin yarda ne na tsawon shekara 20 da ake rikici a gabashin Kongo, inda ake rasa kulawar asibiti ta gari. A wasu wuraren ma ba a samu baki daya.”

Tattaunawa tsakanin al’ummomi

Ma’aikatan lafiya dai na tattaunawa da shugabbanin al’ummomi domin kawar da rashin yardar.

Hakkin mallakar hoto
WHO/

Image caption

Za a iya samun mutane da ke zaune a yankunan karkara ta hanyar rediyo da kuma cibiyoyin sadarwar kauyukansu

“Ya kamata mu saurari damuwar mutane kamar yadda muke so mu ma a ji tamu. Amsoshin da za mu samu kuma za mu yi amfani da su wajen biyan bukatunsu ta fannin lafiya,” a cewar White.

Sannan kuma ta ce za su iya yin nasara.

“Ba zai yiwu mutane su yarda da kai don ka shiga al’ummarsu so daya ba ka tattauna da su kan Ebola. Dole sai ka dauki lokaci wajen samun su yarda da kai tukunna.”

Wannan gaskiya ne musamman idan muka dubi lamarin Charles Lwanga-Kikwaya, wani ma’aikacin lafiya. An kai wa tawagarsa hari a ranar farko ta wannan shekara a wata cibiyar da ake yi wa mutane riga kafi da ke DRC.

Hakkin mallakar hoto
WHO

Image caption

Charles Lwanga-Kikwaya ya yi alwashin ci gaba da kokari har sai an dakile cutar baki daya

Bayan da ya yi kwanaki shida a asibiti yana karbar kulawa mai tsanani, an sallame shi daga asibiti. Bayan wasu ‘yan watanni har ya koma aiki da tawagarsa masu rajin dakile Ebola.

“Zan ci gaba da aiki har sai an dakile cutar baki daya,” in ji Mista Lwanga-Kikwaya.

“Ba zan yarda abokanaina da kannena mata da maza su rasa rayukansu sakamakon cutar da zan iya yin kokari na wajen dakile ta ba,” ya shaida wa WHO.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...