Yadda lalacewar makarantu ke cikas ga ilimin boko a Kano

Makarantu da dama sun lalace a cikin kauyuka

Daya daga cikin matsalolin da ke damun ilimi a Najeriya shi ne lalacewar makarantu, wato gine-ginen da ake amfani da su wajen koyar da yara karatu.

Arewacin Najeriya, shi ne yankin da ya fi yawan yara da ba su zuwa makaranta a Najeriya. Sai dai jihohin da dama suna daukan matakan ganin sun rage matsalar ta hanyar samar da dokoki wadanda ke tilasta wa iyaye sanya yaransu makaranta.

Kano na daya daga cikin jihohin da suka dauki wannan mataki, inda a watan Nuwamba na shekara ta 2020 gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar tilasta wa yara samun ilimi kyauta a jihar.

Sai dai daya daga cikin matsalolin da ake ganin za su yi zagon kasa ga wannan doka shi ne rashin kyakkyawan muhalli na koyarwa.

Duk da kuwa cewa kwamishinan ilimi na jihar Muhammad Sanusi Kiru ya shaida wa BBC cewa jihar ce a sahun gaba wurin kashe wa ilimi kudi a fadin Najeriya.

Ya shaida wa BBC cewa a karshen shekara 2020 an bai wa kowace karamar hukuma ta jihar kudi Naira miliyan 20 domin ta gudanar da aikin gyaran azuzuwa a makarantun firamaren gwamnati.

Wannan a cewarsa kari ne a kan kujerun zama da gwamnatin ta raba a daukacin makarantun jihar.

Haka nan ya ce gwamnatin ta fitar da kudi Naira miliyan dubu daya da dari biyar ta hada da wata Naira miliyan dubu daya da dari biyar domin aikin gina azuzuwa, da kuma samar da sabbin makarantu.

Sai dai BBC ta zagaya wasu daga cikin makarantu a yankunan karkara na jihar domin ganin yadda yanayin makarantun firamaren na gwamnati suke.

A wani kauye da ke karamar hukumar Dawakin Kudu daukacin azuzuwan ba su a cikin yanayi mai kyau.

Makaranta ce da ke a farkon shiga kauyen, ba ta da katanga balle a yi maganar kofar da za a iya kullewa domin hana yara shiga a lokacin da ba a karatu.

Akasarin azuzuwan babu kujerun zama na dalibai, sannan siminti ya farfashe.

Wasu azuzuwan rufinsu ya farfashe, babu murfin kofa, kuma babu murafen tagogi.

Wasu mutanen kauyen da BBC ta tattauna da su sun ce yanayin makarantar na damun su.

Wani mutum mai suna Aminu Idris wanda yaronsa dalibi ne a makarantar ya ce “Gaskiya muna jin abin ba dadi domin kuwa yaranmu sukan zo makaranta da inifom din su amma dole sai sun yi wanki duk bayan kwana daya ko biyu, kayan makarantar ba su dadewa saboda yawan wanki a kullum. Babu abin zama kuma kasan babu dabe.”

Mallam Mato “Abu duk ya tabarbare, kuma wannan rashin kyawu na makarantar nan ya dade a haka, amma tunda muna son ilimin ya za mu yi, ko a rami ne haka za mu tura su.”

A wani kauyen kuma na daban da BBC ta kai ziyara ta ga yadda rufin gini ya rufta cikin azuzuwa, abin da ya sanya da alamu aka daina amfani da azuzuwan guda biyu, a makarantar wadda ke da azuzuwa hudu.

Sauran azuzuwa biyu da suka rage kuma ba su da murafen kofa da na taga, kuma yara ne ke shiga suna wasan kwallon kafa.

Rashin kofofi da tagogi dai ya sa yara na shiga ajjujuwan suna yin kwallon kafa.

A gefen ajujuwan guda hudu na wannan makarantar na ga wata runfa wadda da alama an yi ta ne a matsayin wurin ajiye ababen hawa, amma yaran da na iske sun shaida min cewa nan ma wani aji ne da ake koyar da dalibai.

Mutane da dama wadanda BBC ta tattauna da su a wadannan kauyuka sun ce sun cire tsammani yaransu za su samu wani ilimi mai inganci a nan kusa, duk kuwa da cewa sau da dama sun sha yin nasu bakin kokarin wajen ganin sun magance wasu matsaloli da makarantun fama da su

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...