Yadda aka gudanar da zanga-zangar #RevolutionNow a Najeriya | BBC Hausa

#RevolutionNow
Image caption

Hayaki mai sa hawaye wanda jami’an tsaro suka harba ne ya tarwatsa masu zanga-zangar

A safiyar ranar Litinin, masu zanga-zangar #RevolutionNow suka fantsama kan titunan wasu jihohi domin fara gudanar da gangaminsu wanda suka shirya yi na tsawon ‘yan kwanaki, sai dai da alama abubuwa ba su faru yadda suka so ba.

A cikin makon da ya gabata an kama babban jagoran zanga-zangar wato Omoyele Sowore.

Mai magana da yawun hukumar DSS ya bayyana cewa suke da alhakin kama shi kuma dalilinsu na yin hakan shi ne zarginsa da ake yi na yunkurin hambarar da gwamnati mai ci a kasar.

Omoyele Sowore dai ya yi takarar shugaban kasar Najeriya a zaben da ta gabata kuma shi ne ya shirya zanga-zangar da ya kamata ya faru a cikin jihohi 21 na cikin jihohi 36 na kasar.

#RevolutionNow a Legas

Masu zanga-zangar #RevolutionNow a Legas dai sun bayyana cewa abin da suka gani a yau, lokacin mulkin Shugaba Abacha ne kawai irin lamarin nan ya faru.

A birnin Legas Jami’an tsaro sun watsa hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar tare da kama mutane da kuma duba wayoyinsu, bayan da suka jaddada cewa za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar ta su.

Jami’an ‘yan sanda sun bayyana zanga-zangar ta #RevolutionNow a matsayin cin amanar kasar.

Duk da lamarin da masu zanga-zanga a Legas suka fuskanta da kuma kalaman da jami’an ‘yan sanda suka furta, masu zanga-zangar sun yi alwashin ci gaba da zanga-zangar su a ranar Talata.

Ga hotunan yadda aka gudanar da zanga-zangar a Legas.

Image caption

Sashen Pidgin na BBC na wurin da aka gudanar da zanga-zangar ta #RevolutionNow a jihar Legas

Image caption

‘Yan sanda a birnin Legas

#RevolutionNow a Abuja

A Abuja masu zanga-zanga ba su fito ba, bayan da wakilanmu suka halarci dandalin Unity Fountain inda ya kamata a gudanar da zanga-zangar.

‘Yan sanda dai sun safe suke tururuwar zuwa Unity Fountain domin sanya ido kan abin da zai iya faruwa.

Haka zalika tun safe dai ake ta fama da ruwan sama a Abuja, lamarin da ake ganin cewa yana cikin abubuwan da ya hana mutane halartar zanga-zangar.

Daga baya dai BBC ta samu labarin cewa masu zanga-zanga sun garzaya ofishin hukumar kare hakkin dan Adam da ke Abuja.

Wakilinmu Ibrahim Isa wanda ya je ofishin hukumar ya bayyana cewa mutanen da suka kai kokensu hukumar ba su wuce su uku ba.

Image caption

Unity Fountain Abuja

  • Wole Soyinka da Buhari na musayar yawu kan kama Sowore
  • Mun kama Sowore kan yunkurin kifar da gwamnati – SSS

#RevolutionNow a Fatakwal

Daya daga cikin masu zanga-zangar #RevolutionNow a Fatakwal dai Solomon Lenu ya bayyana wa sashen Pidgin na BBC cewa ba za su ci gaba da zanga-zangar a birnin da ke kudancin Najeriya ba saboda yadda ‘yan sanda suka mamaye ko ina tare da kuma hana mutane zuwa inda ya kamata su aiwatar da zanga-zangar tasu.

Ya bayyana cewa sun yi kokarin shawo kan ‘yan sandan da su ba su damar ci gaba da zanga-zangar.

A jihar Kano kuwa, da ke arewacin kasar ba wanda ya halarci inda aka shirya yin zanga-zangar wato filin wasa na Sani Abacha.

Sashen Pidgin na BBC ya zagaye Kano din kuma jihar na cikin kwanciyar hankali kuma babu jami’an tsaro sosai kamar yadda aka jibge su a sauran jihohi.

Martanin ‘yan Najeriya

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shi ma ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin a shafinsa na Twitter.

Shugaban ya ce “Ba su damar gudanar da zanga-zangar, zai ba su damar kiran kansu shugabanni.”

Wata tsohuwar minista a kasar kuwa, Dokta Oby Ezekwesili ita ma ta mayar da martani kan lamarin.

“Na karanta yadda mutane suka dauki lamarin nan na #RevolutionNow, kuna tsoron Sowore zai hambarar da Shugaba Buhari ne? Kai,Kai!” in ji ta.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...