Yadda aka gano yaran Kano bakwai da ake zargin an sayar a Anambra

Gwamna Ganduje

Bayanan hoto,
A 2019 ne Gwamna Ganduje ya nada kwamitin da zai yi bincike kan yaran da aka sace

Gwamnatin Kano da ke arewacin Najeriya ta ce an gano ƙarin yara bakwai da ake zargin an sace su daga jihar sannan aka sayar da su a jihar Anambra da ke kudancin ƙasar.

Kwamishinan yaÉ—a labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya shaida wa BBC cewa tuni wasu iyaye biyar suka gane ‘ya’yansu cikin yaran da aka gano.

Kwamitin da jihar Kano ta kafa wanda ta É—ora wa alhakin gano yaran da ake yawan sace wa a jihar ne ya kai wata ziyarar jihohin Enugu da Anambra gidan rainon yara, kuma a can ya gano waÉ—annan yara.

“An É—auki hotuna da bidiyon waÉ—annan yara aka yaÉ—a kuma iyaye biyar suka ce sun gano yaransu cikin waÉ—anda suka gani a bidiyon,” in ji Muhammad Garba.

Ya ce har yanzu ana ci gaba da tantance gaskiyar masu da’awar cewa yaran nasu ne saboda kar a yi gudun gara a faÉ—a gidan zago.

Kwamishinan yaɗa labaran ya ce gwamnatin Kano da wannan kwamitin za su yi tsari mai kyau wajen tabbatar da cewa an karɓo waɗannan yara ba tare da jimawa ba.

Akwai wasu rahotanni da ke cewa an ƙara gano wasu yaran jihar guda tara a Jihar Gombe da ke arewacin ƙasar, sai dai Kwamishinan bai tabbatar da labarin ba, ya dai ce matukar aka tabbatar yaran jiharsu ne to su ma za a je a karɓo su.

Iyayen yaran da ake zargin sacewa sun kafa wata ƙungiya ta neman yadda za a yi a dawo musu da yaransu a hukumance, a baya ma har zanga-zangar iyayen yaran mata suka yi wadda kuma ta ƙara wa kwamitin da aka kafa ƙaimi wajen tashi tsaya a nemo yaran.

Ibrahim Isma’il shi ne shugaban Æ™ungiyar iyayen yaran, ya kuma shaida wa BBC farin cikinsa da wannan ci gaba da aka samu.

“Mun ji daÉ—in gano waÉ—annan yara kuma biyu ne cikin bakwai da ba a kai ga samun iyayensu ba, a yanzu haka muna neman yara 113,” in ji Ibrahim Isma’il.

Tun bayan kafa kwamitin na jihar Kano a watan Oktoba an gano wasu yara 9 da aka yi safarar su zuwa jihar Anambra aka kuma sauya musu suna da kuma addini.

Bayan shafe kusan watannin uku zuwa huɗu, kwamitin ya miƙa rahotansa na bincike ga gwamnatin a watan Maris na 2020, wanda ya bayar da shawarwari guda 46.

Sai dai gwamnatin ta ce kwamitin ne ya kamata ya aiwatar da shawarwarin da ya zayyana cikin rahotan nasa wani nauyi da aka ƙara dora masa a karo na biyu.

A shekarar ta 2019 ne, rudunar ‘yan sanadan jihar Kano ta ce ta kama wani mutum mai suna Paul da matarsa Mercy Paul da zargin safarar yara guda 9 zuwa jihar Anambra, inda aka sayar da su aka kuma sauya musu addini.

Amma daga bisani gwamnatin Kano ta karɓo yaran tare da dawo da su hannun iyayensu.

Wasu na danganta batun É“atan yaran da ake samu a jihar da sakacin iyayensu, amma wasu na da ra’ayin akwai sakacin hukumomi wajen tabbatar da doka da oda da kuma kare hakkin al’umma.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...