Yadda Aisha Buhari Ta Kalubalanci Mijinta Da Wakar Adam Zango

Aisha ta wallafa wani dan gajeran bidiyo mai tsawon dakika 22 a karshen mako nan, inda ta rubuta mau’du’in #Achechijama’a, bidiyon da aka hada dauke da sabuwar wakar fitaccen jarumi kuma mawaki Adam A. Zango mai taken “Arewa Na Kuka.”

Wasu da dama na kallon sakon na Aisha a matsayin kalubale ga gwamnatin shugaba Buhari.

Bidiyon ya nuna hotonun Buhari da hafsoshin sojin kasa suna taruka a lokuta daban-daban wasu kuma an nuna shugaban a taron majalisar zartarwar kasar yayin da sautin wakar ta Zango ke bugawa a bayan fagen bidiyon.

A lokacin hada wannan rahoto, mutum dubu 421 suka kalli sakon bidiyon a shafin uwargidan shugaban kasar, mutum 5,499 suka yi tsokaci, dubu 13.14 suka sake wallafa sakon sannan dubu 16.6 suka nuna kaunarsu.

A karshen makon nan Zango ya fitar da wakar wacce ke dauke da baitukan neman hukumomi su kai wa yankin arewacin kasar dauki.

“Arewa na kuka, ana zubar da jininmu, ana kashe al’umarmu, don Allah a kare mu, don Allah a tausaya.” Amshin wakar ta Zango mai tsawon minti uku da dakika biyu take cewa, wacce ya wallafa a shafinsa na Youtube a karshen makon nan.

Har mutum dubu 29 sun kalli wakar a shafin na Youtube cikin kwana biyu a daidai lokacin hada wannan rahoto.

Tuni mawakin ya shiga shafin na Aisha Buhari ya kwafo sakon bidiyon da ta wallafa a shafinta na Twitter @aishambuhari ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Baya ga rikicin Boko Haram da arewa maso gabashin Najeriya ya jima yana fama da shi, hare-haren ‘yan bindiga a arewa maso yammacin kasar ya halaka daruruwan mutane tare da barnata dukiyoyi da dama. Dubbai sun rasa muhallansu.

Amma gwamnati ta tura tarin jami’an tsaro a yankunan jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto a wani mataki na dakile hare-haren.

Wannan matsaya da uwargidan shugaban ta dauka na jan hankalin hukumomi, na zuwa ne yayin da ake jerin zanga zangar neman a rusa rundunar ‘yan sanda ta SARS da ke yaki da masu fashi da makami yayin da wasue jerin zanga zangar ke gudana a arewacin Najeriya wacce take neman kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga.

Wannan ba shi ne karon farko da Aisha Buhari ke fitowa tana kalubalantar gwamnatin mijin nata ba, a shekarar 2016 ta taba furta cewa wani gungun takaitattun mutane ya mamaye gwamnatin Buhari – alamar da ke nuna cewa ba ta gamsu da yadda ake gudanar da al’amura ba.

Ya zuwa wannan lokaci, gwamnatin ta Buhari ba ta ce uffan ba kan sakon da uwargidan shugaban kasar ta wallafa.

More News

Matan APC Sun Ce A Shirye Suke Su Rike Muhimman Mukaman Siyasa A Najeriya A Zabe Mai Zuwa

Jiga-jigan mata mambobin jam’iyyar APC mai multi ciki har da uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, sun ce suna shirye tsaf don jan ragamar mulki...

Yadda matasa suka ƙona makarantar su Hanifa

An cinna wa makarantarsu marigayiya Hanifa wuta da misalin karfe daya na dare a ranar Lahadi, wani ganau ya shaida. Ya kuma ce babu...

Zaben 2023: Ko Tafiyar Win-Win Za Ta Iya Cin Zaben Gwamna A Kano ?

Win-Win Kano Sabuwa tafiyar ta matasa ce" wadannan sune kalaman, Engr Muazu Magaji Dansarauniya jagoran tafiyar gidan  siyasar da ake wa lakabi da Win-Win...

An matsa wa gwanatin Ganduje lamba ta yi dokar kare yara.

Kungiyoyim fararen hula a jihar Kano da ke arewacin Najeriya na ci gaba da matsin lambar neman gwamnatin Ganduje ta samar da dokar da...