Ya kamata Sarki Sanusi ya nemi gafarar Ganduje – Magoya bayan Ganduje

Ganduje da Sanusi

Tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Muhammad Garba, ya mayar da martani ga wasikar da Farfesa Jibrin Ibrahim ya aike wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ja hankalinsa tare da sukar matakan da ya dauka na rarraba Masarautar Kano da kuma takun-sakar da yake yi da Sarki Sanusi.

Wasikar dai ta ja hankalin jama’a da dama, abin da ya sa tsohon kwamishinan wanda na hannun damar Ganduje ne ya mayar da martani, wanda aka wallafa a wasu jaridun Najeriya:

Bayan da gwamnatin jihar Kano ta samu rahoton Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da korafe-korafen al’umma ta jihar, kan sakamakon binciken almundahana da ake zargin Masarautar Kanon da yi, karkashin jagorancin Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, ta aika sakon neman jin bahasi ga Sarkin ta ofishin sakataren gwamnatin jihar ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni.

Inda ta bukaci Sarkin ya yi bayani kan zarge-zargen da ake masa, da zummar saurarensa bisa adalci kafin daukar wani mataki.

Idan za ku tuna, wata kungiya da aka fi sani da ‘Concerned Friends of the Kano Emirate’ ta aika wa hukumar da ke yaki da cin hanci ta jihar wasika tana zargin cewa masarautar Kano ta yi almubazzaranci da Naira biliyan 3.4 wajen siyan abubuwa daban-daban da goyon bayan Sarkin.

Hukumar ta kwashe shekara uku tana duba wannan batu; kuma sai kwanan nan ta kammala binciken, sannan ta yi ta mika sakamakon binciken ga gwamnatin jihar Kano.

Hakkin mallakar hoto
TANKO YAKASAI

Abin dubawa a nan shi ne, hukumar mai yaki da cin hancin mai zaman kanta, na aiki ne da ka’idojin dokar hukumar ta 2008 wato Kano State Public and Anti-Corruption Commission Law 2008.

Shugaban hukumar, Barrista Magaji Rimingado ya bayyana wa ‘yan jarida ranar 10 ga watan Yuni cewa, : ”Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, bai yi katsalandan a binciken ba, kuma ba zai taba yi ba. Ya nuna cewa bisa tanadin da bangare na 8 na kundin tsarin hukumar yaki da cin hancin, wanda ya ayyana hukumar ta yi aiki ba tare da an yi mata ko wane irin kutse ba.

Don haka, duk wani wanda ya san yadda ake tafi da harkokin gwamnati ba zai soki takardar neman bahasi ga Sarki Muhammadu Sanusi da gwamnatin jihar kano ta mika masa ba.

Sai dai abin mamaki, Sarki Sanusi ya bi ka’ida ya amsa takardar ya kuma bayar da bahasin.

A bisa haka ne, na yi mamakin dalilin wata makala da aka buga a shafin karshe na jaridar Daily Trust ta Juma’a 7 ga watan Yuni mai taken “Wasika zuwa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.”

Marubucin makalar, Jibrin Ibrahim ya bukaci Gwamna Ganduje ya janye neman bahasin, inda a ra’ayinsa, ya ce bai kamata a bayar da takardar neman bahasin ba ma tun farko!

Haka kuma, takardar neman bahasin ta soki kirkirar Masarautar Bichi da sabunta wasu masarautun na Gaya da Rano da Karaye inda ya bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na rage tasirin Sarki Sanusi.

Jibrin ya danganta wannan da abubuwan da suka biyo bayan kirkirar masarautu hudu na Auyo da Dutse da Gaya da Rano da marigayi Abubakar Rimi ya yi ranar 1 ga Afrilu na 1981.

Sai dai abin dubawa a nan shi ne tsohon Gwamna Rimi ya kirkiri wadannan masarutun ne ba tare da taimakon majalisar dokokin jihar ba, da sauran abubuwan da suka kunshi kirkirar masaurautu, wanda Abdullahi Ganduje ya bi daki-daki kafin sabunta masarautun Karaye da Gaya da Rano da kuma kirkirar Bichi.

Ya kamata Jibrin ya tuna cewa, ba Gwamna Ganduje ne ya assasa kirkirar sabbin masarautun ba. Haka kuma ba shi ya kai maganar majalisar jiha ba. Abin kawai da ya yi shi ne yin aikin da ya rataya a wuyansa na sa hannu kan doka.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An kirkiri sabbin masarautun hudu wato- Rano da Gaya da Bichi da Karaye

”Idan za a tuna, Mista Ibrahim Salisu Chamber ne ya bayar da shawarar a kirkiri sabbin masarautun wanda ya ce a ba su kima daya da Masarautar Kano. A ganinsa, kirkirar sabbin masarautun zai kawo ci-gaba a jihar.

Ya jaddada cewa hakan zai janyo mutane kusa da gwamnatin jihar, kuma a cewarsa wannan zai tabbatar da tsaro a jihar.

Bari in dan mayar da mu baya mu duba tarihi. Daliban tarihi za su san cewa masarautar Gaya ta girmi ta Kano a zahiri.

Daga farko, makeran Gaya sun fara yada zango ne a Dutsen Dala lokacin da suke neman karfe.

Zamansu a nan ya sa kananan unguwanni suka kafu jefi-jefi, kuma daga baya suka zama garin Kano. Ko da aka yi Jihadin Dan Fodio, Gaya ta ci gaba da zama masarauta mai cin gashin-kanta. Sai dai a shekarar 1914, Turawan mulkin mallaka suka rage wa masarautar girma aka mayar da ita gunduma.

Masarautar Karaye kuwa ta dade da kafuwa, tsawon daruruwan shekaru a matsayin masarauta mai zaman kanta. Ita ma ko bayan Jihadin ta ci gaba da cin gashin-kanta, sai dai Turawan mulkin mallaka sun rage mata karfi zuwa gunduma.

An kafa Masarautar Rano tun shekara ta 1000 A.D kalandar miladiyya.

Ita ma dai masarauta ce mai zaman kanta kuma sarakuna da yawa sun mulke ta. Kuma Rano na cikin sanannun kasashen Hausa da a tarihi ake ce wa Hausa Bakwai, wadanda Bagauda ya kafa.

Sai dai kamar sauran masarautun, Turawan mulkin mallaka sun cire Rano daga matsayin masarauta a shekarar 1908.

Ita kuwa sabuwar masarautar Bichi, an kwashe shekaru ana kokarin kafa ta. Kuma matsayinta da girmanta a jihar Kano ya sa ta cancanci a bata masarauta.

Don haka abin takaici ne, mutum kamar Jibrin Ibrahim ya zama mai kira a yi tashin hankali a Kano don shi da iyalinsa ba a nan suke da zama ba.

Kuma ba kamar yadda ya ce ba ne, don kuwa babu zaman dar-dar a Kano tun 8 ga watan Mayu don ko mazauna garin da baki ma za su shaida cewa babu tashin hankali ko wani zaman dar-dar a jihar, kamar yadda take tun hawan Gwamna Ganduje mulki ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Ko a lokutan da makwaftan jihar ke fama da rikice-rikice, Kano ta ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ya kamata Jibrin Ibrahim ya gane cewa an wuce lokacin daukar matasa masu zaman kashe-wando don bangar siyasa, yayin da ‘ya’yansu ke kasashen waje suna karatu.

Shirye-shiryen gwamnati na taimaka wa matasa, da manufofin samar da ilimi kyauta da gwamnatin Ganduje ta kaddamar sun samar wa matasanmu mafita daga wannan aikin wahalar.

Jibrin Ibrahim ya sani cewar wannan wani sabon babi ne, kuma dole ne Kano ta dau hanyar sauyi ita ma.”

Hakkin mallakar hoto
DAILY NIGERIAN

Image caption

Farfesa Jibrin Ibrahim

”Bai kamata a sauya manufar kirkirar sabbin masarautu a Kano ba, zuwa cewa ana so a tarwatsa masarautar Kano da martabarta ba.

Kawai wani mataki ne na fadada al’adun Kano da kuma kai ci gaba ga mutane. Sabbin masarautun Bichi da Gaya da Rano da Karaye sun kafu kenan.

Babu abin da Gwamna Ganduje zai iya yi ya sauya hakan. Doka ce ta ce haka. Shugaba kuma dan-kasa mai bin dokoki irin Gwamna Ganduje ba zai iya maida hannun agogo baya ba kan sabbin masarautun.

Daga karshe, dole a jinjina wa ‘yan Najeriya da suka taka rawa wajen yin sulhu tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba, Sarki Muhammadu Sanusi na biyu. Wannan mataki ne da Gwamna Ganduje mai son zaman lafiya zai karba hannu bibbiyu.

Sai dai fa kamata ya yi Sarki Sanusi ya bai wa Gwamna Ganduje da daukacin al’ummar Kano hakuri a bayyane, bisa kunyata masarautar Kano da yayi da kuma cakuda ta da siyasa.

Haka kuma, mutuncin Sarki Sanusi shi ne ya janye duk wata karar gwamnatin jihar Kano da aka kai da yake tallafawa.

Wannan zai nuna matsayinsa na son zaman lafiya da yafiya don ci gaban Kano da al’ummarta.

Abu mafi muhimmanci shi ne, Sarki Sanusi ya janyo sarakunan Karaye da Rano da Gaya da Bichi jikinsa, kuma ya nuna cewa a shirye yake ya hau matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar Kano.

Haka kuma, ana sa rai zai yi amfani da kwarewarsa ya koyar da sauran sarakunan, ya kuma tabbatar da cewa sun yi dukkan mai yiwuwa wajen ciyar da jihar Kano gaba.

A lokacin da aka yi duka wannan ne, sulhun zai kayatar kuma ya zama mai riba.”

Malam Muhammad Garba shi ne tsohon Kwamishinan watsa labarai da matasa da al’adu na jihar kano.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...