Ya kamata gwamnati ta raba wa talakawa abinci gida-gida – Dattijan Arewa

Tasawirar arewacin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tasawirar arewacin Najeriya

Kungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta soki tsarin da gwamnatin kasar ke bi wajen bai wa al’umma tallafi bayan rufe wasu jihohin kasar ciki har da babban birnin Abuja da jihar Legas inda cutar koronabairus ta fi kamari a kasar.

Mai magana da yawun kungiyar Northern Elders Forum, Dr Hakeem Baba Ahmad ya shaida wa BBC cewa matakin gwamnati na rufe jihohin ya zo a gaggauce saboda ba a ba da isasshen lokaci ga al’umma su yi tanadin abinci na tsawon lokacin da za su zauna a gidajensu ba.

“Inda muka ga an yi kuskure (shi ne) an yi jawabi karfe shida na yamma, an ce kada wanda ya sake fita daga karfe 12 na dare, an ce hujjar gwamnati ita ce ta hango mummunar masifa da ke tahowa.” kamar yadda Dr Hakeem ya bayyana.

Ya kara da cewa bai kamata gwamnati ta tsare mutane, ba tare da an yi musu tanadin yadda za a sama musu abinci ba.

Ya ce “ba a yi tanadin abinci ba aka kulle mutane, akwai mummunar yunwa, yawancin mutane a arewa da sauran Najeriya, wasu abincin da za a ci a gidajensu sai sun fita, sun nema,”

“Abincin gobe, babu shi yau, idan ka kulle mutum gaba daya, ba a fita yau ba, ba a fita gobe ba, kuma ba shi da shi, idan ya kwana daya, ya kwana biyu, ya kwana uku sai mutum ya fara karya doka,” in ji Dr Hakeem Baba Ahmed.

A cewarsa tsarin rarraba naira dubu ashirin-ashirin ga marasa karfi bai wadatar ba saboda su “kalilan ne a cikin mutane”. “Ana maganar yunwa ne a kasa gaba daya, mutane cikin miliyan dari biyu, ba mu ce a ba (duk) mutane miliyan dari biyu abinci ba,”

Hakkin mallakar hoto
@ProfZulum

“Amma akwai talaka wanda ba shi da shi kuma gwamnati ba ta da rajistarsa, ba ta da sunansa, a dauko abincin nan daga Abuja a kai jihohi, jihohi su kai kananan hukumomi, kananan hukumomi kuma su kai mazabu,” in ji shi.

A ganinsa, kamata ya yi a kafa kwamitin nagartattun mutanen da aka yarda da su kuma masu tsoron Allah “a mika musu abincin a ce tsakaninsu da Allah su bi gida-gida su rarraba wa mutane ta yadda za su samu abin kai wa bakunansu.”

Dr Hakeem Baba ya kuma ce akwai bukatar gwamnati ta tabbatar ta yi amfani da tallafin da ta samu daga daidaikun jama’a da kuma bankuna ta hanyar da ta dace.

Ya bayyana cewa babu wani alfanu idan gwamnati ta yi tanadin magungunan yaki da annobar coronavirus ba tare da bai wa mutane abinci ba, idan har ta kai jama’a sun yi bore ko sun mutu.

Mai magana da yawun dattijan ya kuma gargadi ‘yan kasuwa a kan kara farashin kayan masarufi tare da bai wa al’umma hakuri kan halin da suka tsinci kansu a ciki.

A cewarsa, “abin da muke gudu mun hango ne kada mutane su tunzura har ya kai ciwo zai zama cuta.”

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...