Ya kamata Afirka ta shirya zuwan mummunar annoba — WHO

Wani jami'in lafiya na gwada zafin jikin mutane a filin jirgin saman kasar Habasha

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Africa ana gwaji a yawancin filayen jiragen sama na kasashen Afirka

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce yakamata Afirka ta tashi tsaye don tunkarar munin halin da za a shiga sakamakon annobar coronavirus tare da shirya yaki da ita.

Ya kamata nahiyar ta lura da yadda cutar ke saurin yaduwa in ji Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Shugaban ya yi gargadin cewa duk da kasancewar babu masu fama da cutar sosai a nahiyar, amma ya kamata a dauki matakin da ya dace wajen hana yaduwarta.

Mr Ghebreyesus ya ce ” Afirka ku tashi, nahiyata ku farka domin dakile yaduwar coronavirus”.

Kwararru a bangaren lafiya sun yi gargadin cewa matsalar da kasashen Afirka ke fama da ita ta rashin isassun kayayyakin kula da marasa lafiya na iya ta’azzara idan cutar ta ci gaba yaduwa musamman a wajen taron jama’a.

Hukumar lafiya ta duniyar ta bayar da shawarar a guji shiga tarukan jama’a.

A Afirka, ya zuwa yanzu mutum 16 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus inda mutum 6 suka fito daga kasar Masar, 6 daga Algeria, biyu daga Morocco daya a Sudan sannan daya a Burkina Faso.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tedros Adhanom Ghebreyesus

A Afirka ta Kudu, inda aka samu mutum 116 da suka kamu, shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya ayyana cewa ana cikin babban bala’i saboda bullar covid-19, don haka ya takaita tafiye-tafiye, aka kuma rufe makarantu, da hana taruka tare da rufe gidajen barasa.

Kazalika kasar ta kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa.

An sanya hukuncin zaman gidan yari ko biyan tara a Afirka ta Kudu ga duk wanda ya karya ka’idojin da aka shimfida na yaki da coronavirus a kasar.

Akwai wasu kasashen Afirkan da su ma suka sanya takunkumai makamantan na Afirka ta Kudu.

Jihar Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya, ta haramta gudanar da tarukan da suka wuce na mutum 50, sannan za a rufe makarantu daga mako mai zuwa.

Kazalika Najeriya ma wadda ya zuwa yanzu take da mutum 12 da suka kamu da cutar, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga kasashen da cutar ta yi kamari.

Ita kuwa Algeria, wato daya daga cikin kasashen Afirkan da cutar ta fi yawa, ta rufe dukkan iyakokinta sannan ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Haka an haramta gudanar da tarukan jama’a a kasar.

Rwanda, wadda ke da mutum 11 da suka kamu da cutar za ta hana shiga kasarta daga ranar Jumma’a 20 ga watan Maris har tsawon wata guda.

Kenya, ta dakatar da sallah a masallatai tare da hana gudanar da ibada a majami’u, sannan kasar ta ce za ta samar da sinadarin goge hannun don rabawa kyauta ga ‘yan kasar.

Liberia, wadda ta sha fama da cutar Ebola a shekarun baya, tana da mutum biyu da suka kamu da coronavirus, kuma ta hana bayar da visa domin dakatar da tafiye-tafiye a tsakanin ‘yan kasar.

Kazalika ta hana ‘yan wasu kasar shiga kasarta.

Zambia, wadda ke da mutum biyu da suka kamu da cutar ta dakatar da taron majalisun kasar tare da rufe makarantu da jami’o’i.

Somalia mai mutum guda ta rufe sararin samaniyarta.

Uganda da Botswana ba su samu bullar cutar a kasashensu ba ya zuwa yanzu amma duk da haka za su rufe makarantu daga mako mai zuwa.

Chadi wadda aka samu mutum guda da coronavirus ta harba, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen fasinja tare da kulle iyakokinta na tudu.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...