Wolverhampton ta gano barakar Man City | BBC Sport

Man City

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Wolverhampton da ci 2-0 a wasan mako na takwas da suka fafata a gasar Premier ranar Lahadi a Ettihad.

Wannan ne karon farko da Wolverhampton ta ci Manchester City a babban wasan tamaula tun bayan 1979.

Kuma Wolverhampron ta ci kwallon farko ta hannun Adama Traore saura minti 10 a tashi daga wasan, kuma shi ne ya kara na biyu daf da za a tashi daga karawar.

Kawo yanzu City ta barar da maki biyar a gida a wasa hudu a bana, bayan da a bara uku ta rasa a kakar da ta lashe kofin Premier.

Kawo yanzu Liverpool wadda take ta daya a kan teburin Premier ta bai wa City wadda take ta biyu tazarar maki takwas a kakar bana.

City ta buga 2-2 da Tottenham a Ettihad a wasannin bana, haka kuma ta yi rashin nasara a hannun Norwich City da ci 3-2 a gasar ta Premier.

Wolverhampton tana mataki na 12 a kan tebrurin Premier da maki 10.

Manchester City za ta ziyarci Crystal Palace a wasan mako na tara a gasar ta Premier ranar 19 ga watan Oktoba.

Ita kuwa Wolverhampton za ta karbi bakuncin Southampton a wasan mako na tara ranar ta 19 ga watan Oktoba.

More from this stream

Recomended