Connect with us

Hausa

WhatsApp ya gano leken asiri da ake yi wa mutane da shafinsa

WhatsApp logo

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An tabbatar da cewa masu kutse na iya jefa manhajar tattara bayanan sirri daga nesa cikin wayoyi da sauran na’urorin shiga intanet ta hanyar yin amfani da wata babbar tawaya da aka gano a manhajar aika sakwanni ta Whatsapp.

Kamfanin WhatsApp, wanda mallakar Facebook ne, ya ce ana hakon wasu “zababbun mutane” da ke amfani da kafar sada zumunta, kuma “wani jigo cikin harkokin fasahar intanet” ne ya yi sanadin hakan.

An kaddamar da gyare-gyare tun ranar Juma’a.

A ranar Litinin kuma kamfanin WhatsApp ya bukaci dukkan masu amfani da shafinsa mutum biliyan daya da rabi su sabunta manhajojinsu don karin kandagarki.

An fara ba da rahoton wannan al’amari wanda aka gano a farkon wannan wata ne a cikin jaridar Financial Times.

Ana amfani da fasahar kira ta Whatsapp a buga wa wayar mutumin da ake hako. Kuma ko bai amsa kiran ba, manhajar tattara bayanan za ta makale wa wayarsa, kuma kamar yadda aka ba da rahoton kiran zai bace daga jerin kiraye-kirayen wayar.

  • An kama mai kula da dandalin WhatsApp da matan aure a Kano

WhatsApp ya fada wa BBC cewa jami’an tsaronsa ne tun farko suka gano tangardar, kuma suka yi musayar bayanai da kungiyoyin kare hakkin dan’adam da wasu kwararru kan sha’anin tsaro da kuma Ma’aikatar Shari’ah ta Amurka a farkon wannan wata.

“Harin na da duk siffofin wani kamfani da aka ba da rahoton yana aiki da gwamnatoci wajen safarar manhajojin leken asiri da ke kwace ragamar ayyukan wayoyin salula,” kamfanin Whatsapp ya bayyana ranar Litinin cikin wata sanarwa ga manema labarai.

Jaridar Financial Times ta ba da rahoton cewa kamfanin tsaron Isra’ila na NSO Group wanda a baya ake bayyana shi da “dillalin makaman da ake harbawa ta intanet” ne ya kirkiro wannan hari.

Sai dai a cikin wata sanarwa kamfanin ya ce: “Fasahar NSO an ba ta lasisi don bai wa hukumomin gwamnati iko, bisa manufar yaki da aikata lafiuka da ta’addanci”.

WhatsApp ya ce ya yi wuri a san adadin masu amfani da shafinsa da wannan tawaya ta shafa, ko da yake ta kara da hare-haren da ake zargi ana kai su ne kan manyan jiga-jigai.

A cewar alkaluman baya-bayan nan na Facebook, masu amfani da shafin WhatsApp sun kai biliyan daya da miliyan 500 a fadin duniya.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya | BBC Hausa

Zababbun hotuna daga fadin Afirka a wannan makon:

A boy reading the Koran - Sunday 12 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wani yaro musulmi yana karatun Kur’ani a Al-Kahira, Masar ranar Lahadi yayin watan azumin Ramadan…

A large number of people sitting inside a mosque waiting to break the fast - Sunday 12 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Duk dai a rana guda, musulmai sun taru don zagayowar ranar da aka bude masallacin Al-Azhar a Al-Kahira karo na 1079 kafin su yi buda baki.

three men share a bottle of water - Monday 13 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Can a tsibirin Ibo na Mozambique, wasu Musulmai suna raba ruwa don yin buda baki daf da faduwar rana, ranar Litinin.

Protesters wave the Algerian flag beneath a shower of water - Friday 10 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ranar Jumna’a, masu zanga-zangar neman sauyi na daga tutar Algeria a lokacin da ake yayyafi a babban birnin Algiers.

Three somali women putting food into small take away containers - Wednesday 15 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yayin da wasu mata ‘yan Somaliya suka nannade hijabansu don shirya abincin buda bakin da kungiyar agaji ta kasar Turkiyya ta samar a Mogadishu ranar Laraba.

A mother carrying a bag on her head and a baby on her back - Saturday 11 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wata mata ta murmusa a lokacin da take goye da jaririyarta a birnin Harare, Zimbabwe ranar Asabar.

A large group of people dancing with a

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Magoya bayan Lazarus Chakwera, shugaban jam’iyyar Congress Party a Malawi na rawa a babban birnin Lilongwe ranar Lahadi.

Three children seen through the broken window of a bus - Friday 10 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

To sai dai a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ranar Juma’a, yanayin ba na farin ciki ba ne inda ake hangen yara uku ta wata fasasshiyar tagar motar bas mai dauke da ‘yan gudun hijirar Sudan ta Kudu daga iyaka zuwa garin Biringi na kasar Congo….

A South Sudanese woman standing in a colourful dress - Saturday 11 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wata mata ‘yar gudun hijira ‘yar Sudan ta Kudu ta nuna atamfar ta mai haske a wani sansanin ‘yan gudun hijira a Biringi na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ranar Asabar.

Presentational white space

Woman plaits a little girl's hair whilst two other women look on

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wata mata ‘yar Zimbabwe na yi wa wata yarinya kitso a babban birnin Harare ranar Litinin.

Mid-shot on legs on a railway track - Sunday 12 May

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wani mai zanga-zanga na tafiya a kan titin jirgin kasa da aka rufe wanda ke zuwa har inda ake gudanar da zanga-zanga a babban birnin Sudan, Khartoum ranar Lahadi.

Hotuna daga: Getty Images

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Abdulaziz Yari a Saudiya

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce zai iya bakin kokarinsa domin ya tabbatar da cewa yan Najeriya sun zauna lafiya.

Mai magana da yawun shugaban kasar Mallam Garba Shehu shine ya rawaito shugaban kasar na fadin haka lokacin da ya yi bude baki tare da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ranar Lahadi a birnin Makka dake ƙasar Saudiyya.

Ya yin buda bakin gwamnan na tare da Sarkin Maradun,Garba Tambari.

Buhari ya tashi daga nan gida Najeriya ranar Alhamis domin aikin Umrah a kasar Saudiyya kuma ana sa ran dawowarsa gida ranar Talata.

A tabakin Garba Shehu shugaban ya bayyana damuwarsa kan asarar rayuka da ta dukiya da ake samu a Zamfara.

nagana da gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

Kano: Masu zanga-zanga sun yi arangama da ‘yan sanda

Dubban masu zanga-zanga da suka fito a kungiyance domin yin Allah wadai da gina wani kamfani mallakar Aliko Dangote, sunyi karan batta da jami’an ‘yan sanda har ma suka tarwatsa su da hayaki mai sanya hawaye.

Acewar al’ummar garin Danmarke dake karamar hukumar Makoda a jihar kano ta bakin Ali Isah Thomas, yace “Ba suyi mamakin afkuwar wannan al’amari ba, saboda rashin kyakkyawar alakar dake tsakanin su da jagororin yankin wanda ba kasafai suke zama suyi mahawara dasu ba aduk lokacin da wani bakon al’amari ya taso don ciyar da su gaba.”

Isah Thomas ya kuma yi zargin cewa a yayin waccan fatattaka, ‘yan sandan sun harbi mutum biyu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sadan Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya karyata zargin harbi da masu zanga-zangar suka ce anyi, sai dai yace a kokarin da rundunar su tayi na ganin sun tseratar da rayuka da tabbatar da bin doka da oda, wannan yasa rundunar ‘yan sanda amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar.

Wakilin Hausa7 Idris Usman Alhassan Rijiyarlemo ya nemi jin bahasi daga shugaban karamar hukumar Makoda Hon. Abubakar Salisu Makoda, don jin ta bakin sa game da zargin chefanar da filin ga Aliko Dangote don gina kamfani, kamar yadda masu zanga-zangar suka koka.

Sai dai har kawo lokacin da wakilin mu ya aiko mana da wannan rahoto bai sami jin ta bakin Hon. Makoda ba.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: