Ana zargin wata mata mai suna Rahimat Salaum da kashe mijinta dake da lalurar shanyewar ɓarin jiki a yankin Pegi dake birnin tarayya Abuja.
SP Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja a cikin wata sanarwa ranar Talata ta ce jami’an ƴan sanda na ofishin rundunar dake Pegi ne suka kama matar a ranar Litinin.
A cewar Josephine matar na ƙoƙarin tserewa ne da kayan mijin nata kafin ƴan sanda suje su kamata.
“Bayan yi mata tambayoyi wacce ake zargin ta amsa laifin kashe mijinta bayan da suka yi faɗa a tsakaninsu. Daga bisani ta yiwa ƴan sanda jagora zuwa wani gini da ba a kammala ba inda ta jefar da gawar da aka ƙone.”a cewar sanarwar.
Rundunar ta ce ana cigaba da gudanar da binciken kan lamarin.