Amarachi Ugochukwu wata ma’aikaciyar banki a Ikorodu dake jihar Lagos ta kashe kanta saboda “matsin rayuwa” kamar yadda ta rubuta.
Matashiyar ma’aikaciyar mai shekaru 32 ta sha guba ne a cikin bankin ranar Litinin.
Wasu majiyoyi dake bankin sun bayyana cewa da misalin karfe 1 na rana ne ma’aikaciyar ta shige banɗaki inda ta sha maganin kwari da ake kira Sniper.
Wani dake amfani da kafar sadarwar X ya wallafa hoton ma’aikaciyar da kuma gubar da tasha a gefenta.
Ma’aikaciyar cikin rubutaccen sakon da ta bari ta ɗora alhakin yin haka kan ” halin matsin tattalin arzikin kasa” ta kara da cewa “ba zan iya jure wannan ciwon ba”.
Ta kuma bawa iyayenta hakuri da kuma sauran yan uwanta.