Wata ƙungiya ta ba wa Atiku shawarar kar ya fito takara a 2027

Wata kungiya a cikin jam’iyyar PDP, CPDPL, mai suna Concerned PDP League, ta yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 da kada ya sake tsayawa takara a 2027.

Shawarar kungiyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa.

Sakatariyar kungiyar ta kasa, Alhaji Tasiu Muhammed da kuma mukaddashin daraktan yada labarai da sadarwa na kasa, Gbenga Adedamola, ne suka sanya wa hannu a ranar Lahad.a Abuja.

CPDPL ta kuma bukaci shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, da kada ya sanya wani buri na neman kujerar shugaban kasa har sai 2031, don kauce wa sake faruwar abin da ya faru da jam’iyyar a 2015 da 2023.

A cewar kungiyar, shawararta ta kasance wani abin tuni ne ga masu sha’awar yin mulki daga Arewa su fahimci cewa Kudu tana da shekaru takwas kafin mulki ya dawo Arewa a 2031.

More from this stream

Recomended