Wani jami’in kwastam ya harbe kansa har lahira a Kano

Wani jami’in hukumar kwastam ya harbe kansa har lahira a gidansa dake unguwar Farm Centre a cikin birnin Kano.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kiyawa ya ce jami’in mai suna Abdullahi Magaji na aiki ne a hedkwatar hukumar ta kwastam dake Abuja ana zargin cewa ya kashe kansa ne a ranar 06 ga watan Mayu.

Babban baturen ƴan sanda na Farm Centre shi ne ya jagoranci jami’an ƴan sanda ya zuwa gidan da abun ya faru.

Tuni dai kwamishinan ƴan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Related Articles