An ga wani malami a jami’ar jihar Benue da ke Makurdi a wani hoton bidiyo yana cin zarafin wani dalibi.
Bayanai dai sun nuna cewa malamin mai suna Mista Ichor Tersagh malami ne mai ziyara a Jami’ar Jihar Benue (BSU) daga Sashen nazarin halittu a Jami’ar Joseph Sarwuan Tarka, Makurdi.
Wasu rahotanni sun ce malamin ya rarranƙwashi dalibin ne saboda ya shigo masa aji lokacin da yake koyarwa.
Sai dai har zuwa yanzu ba jami’ar ba ta ce komai game da wannan zargi ba.