Wane ne sabon Gwamnan Bayelsa, Douye Diri? — BBC Hausa

0
Gwamna Douye Diri

Hakkin mallakar hoto
BAYELSA STATE GOVERNMENT

Image caption

Douye Diri ne gwamnan jihar Bayelsa na biyar a tarihi

Sanaata Douye Diri na jam’iyyar PDP ya zama gwamnan jihar Bayelsa na biyar a tarihi, inda ya shiga ofis bayan hukuncin Kotun Kolin Najeriya da ya sauke Chief David Lyon na jam’iyyar APC, wanda INEC ta ce shi ne ya ci zaben 2019.

Diri ya fito ne daga mazabar Isampou kuma yana wakilcin kananan hukumomin Kolokuma/Opokuma ne a Majalisar Dattawan Najeriya kafin yanzu.

An haife shi ranar 6 ga watan Afrilu na shekarar 1959.

Kafin ya shiga siyasa, Sanata Diri malamin makaranta ne mai shaidar koyarwa ta NCE da ya samu daga kwalejin Rivers State College of Education a shekarar 1985.

A shekarar 1990 ne ya koma makaranta, inda ya yi digiri a fannin koyarwa da kuma siyasa a College of Education, wadda yanzu ta zama jami’ar Ignatius Ajuru University of Education, a Fatakwal.

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK

Ya shiga harkokin siyasa a matsayin babban sakatare na cibiyar Centre for Youth Development daga 2000 zuwa 2002.

Sannan ya zama kwamishinan matasa da wasanni a 2006-2007 karkashin gwamnatin Timipre Sylva.

Sai kuma a shekarar 2008 zuwa 2012 ya zama mamba a majalsar gudanarwa ta jami’ar University of Maiduguri da ke jihar Borno.

A shekarar 2012 ne Sanata Diri ya zama mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati a lokacin Gwamna Henry Seriake Dickson, zuwa 2013 kuma ya zama babban sakataren gwamnan.

Ya zama sanata a 2015 zuwa 2019 mai wakiltar mazabar Kolokuma/Opokuma.

Diri ya lashe zaben Sanatan Bayelsa ta Tsakiya a 2019 kafin daga bisani ya shiga takarar gwamnan jihar karkashin PDP, inda ya fafata da ‘yan takara sama da 20.

A sakamakon zaben gwamnan na 16 ga Nuwamban 2019, jam’iyyarsa ta PDP ta samu kuri’u 143, 172, yayin da APC ta samu 352, 552.

Sai dai Kotun Koli ta soke zaben David Lyon na APC bisa dalilin cewa mataimakinsa ya gabatar da takardun boge ga INEC kafin zaben.

Hakan ya sa APC ta rasa kujerar sakamakon umarnin kotun cewa a bai wa dan takarar da ya zo na biyu a zaben, wanda kuma PDP ce da dan takararta Sanata Douye Diri.

Hakkin mallakar hoto
BAYELSA STATE GOVERNMENT

Image caption

A ranar 14 ga watan Fabarairun 2020 aka rantsar da Douye Diri a mtsayin Gwamnan Bayelsa

A ranar 14 ga watan Fabarairun 2020 ne kuma ya zama gwamnan jihar Bayelsa na biyar a tarihi bayan ya sha rantsuwar kama aiki da kuma ba shi shaidar lashe zabe.

Yana da mata daya mai suna Misis Gloria Diri kuma sun haifi yara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here