Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Afirka Sun Haura 500,000

Hukumar lafiya ta duniya ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka ya haura dubu 500,000, kuma akwai damuwa yayin da karin kasashe ke fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar.

Sanarwar da hukumar ta WHO ta fidda ta ce ya zuwa yanzu, cikin kasa da wata biyar, cutar COVID-19 ta lakume rayuka 11,959, abinda ya haura rayuka 11,308 da aka rasa sakamakon barkewar cutar Ebola mai muni a yankin Afirka ta Yamma tsakamin shekarar 2014 zuwa 2016.

Adadin wadanda suka kamu da cutar ya linka sosai a kasashe 22 na yankin a cikin watan da ya gabata. Kusan kashi biyu cikin uku na kasashen na fuskantar yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

Kasashen Algeria, Masar, Ghana, Najeriya da kuma Afirka ta Kudu suna da kusan kashi 71 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar a nahiyar. Afirka ta Kudu kadai na da kashi 43 cikin 100.

Yayin da cutar COVID-19 ke cigaba da yaduwa, dubban ma’aikatan lafiya sun kamu da rashin lafiya. Samar da kayayyaki da kare ma’aikatan lafiya shine muhimin abu a yaki da annobar COVID-19.

Hukumar WHO na aiki don tallafa wa kasashen da ke yaki da annobar COVID-19 ta hanyar samar da bayanai kan abinda ya kamata su yi, da muhimman kayayyakin aiki, kuma hukumar ta horar da ma’aikatan lafiya sama da dubu 25 daga nesa.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...