Uzodimma ya lashe zaɓen gwamnan Imo da gagarumar rinjaye

Dantakarar jam’iyar APC kuma gwamna mai ci, Hope Uzodimma ya sake lashe zaÉ“en gwamnan da aka yi a ranar Asabar.

Uzodimma ya samu nasara ne da gagarumin rinjaye kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓe ta INEC ta fitar ya nuna.

Gwamnan ya samu nasara da kuri’a 540,308 akan manyan abokanan takararsa na jam’iyar PDP da Labour Party.

Sakamakon ƙananan hukumomin jihar 27 da INEC ta bayyana ya nuna cewa gwamnan ya lashe zaɓen da a dukkanin kananan hukumomin.

Jam’iyar PDP ce tazo ta biyu a zaÉ“en da kuri’a 71,503 sai kuma jam’iyar Labour Party inda É—an takararta Athan Achonu ya samu kuri’a 64,081.

More News

An sake gano gawar wani shugaban Fulani da ya ɓata a jihar Filato

An gano gawar wani Arɗon Fulani, Umar Ibrahim da ya ɓace a cikin wata rijiya dake kauyen Jokom a ƙaramar hukumar Mangu ta...

An kama Æ´an kungiyar IPOB 18 da ake zargi da kisan Æ´an sanda

Rundunar yan sandan jihar Imo ta kama mutane 18 da ake zargi da zama yan kungiyar IPOB da suke da hannu a kisan Æ´an...

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen gwamnan jihar Sokoto

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da zaɓen, Ahmed Aliyu a matsayin gwamnan jihar Sokoto. Rukunin alkalan kotun su uku sun yi watsi da...

Kotun ɗaukaka ta soke zaɓen shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja, ta soke zaɓen kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman. Alkalan kotun uku sun bayar da umarni da a sake...