United na tattaunawa kan yi wa Old Trafford kwaskwarima

Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Old Trafford na daukar ‘yan kallo 74,140

Manchester United na tattaunawa kan fadada filin wasanta na Old Trafford, domin yake daukar ‘yan kallo 80,000.

Ana sa ran wurin zama da ake kira da sunan Sir Bobby Charlton, shine za a yi wa gyare-gyare da dama.
Masu sukar Old Trafford – shine filin da ya fi cin ‘yan kallo a Ingila mai wurin zama 74,140, wanda aka dade ba a gyara ba – ana ta korafin wurin zama da ake kira Charlton Stand na digar ruwa daga saman rufin.
Rabon da a yi wa Old Trafford babban gyara tun 2006.

Tuni dai Manchester City da Arsenal suka koma sabbin filayen wasan da suka gina har da Tottenham a baya-bayan nan.

Liverpool ma na kan hanyar kawata filinta na Anfield, bayan da ta yi masa gyare-gyare a 2016, yanzu tana fatan fadada shi domin daukar karin ‘yan kallo don fuskantar kakar 2023/24.

[ad_2]

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...