Twitter zai dawo aiki a Najeriya bayan haramta shi na tsawon kwana sama da 200

0

Gwamnatin Najeriya ta kawo ƙarshen hanin da ta yi wa ƴan ƙasarta game da amfani da kafar sadarwa ta Twitter.

Wannan na zuwa ne bayan shafe sama da kwanaki 200 ba tare da yin Twitter ba, sai dai ta haramtacciyar hanya.

Shugaba Buhari ya amince da kawo ƙarshen haramcin ne bayan bangaren gwamnatin da na Twitter ɗin sun cim ma matsaya.

Ministan Sadarwa, Dr. Isah Ali Pantami, shi ne ya rubuta w shugaba Buhari cikin wata wasika cewa za a iya dawo da kafar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here