Twitter: Kamfanin ya yi maraba da kalaman Buhari na son cire takunkumin da aka sanya masa

Twriter

Asalin hoton, Getty Images

Dandalin sada zumunta na Twitter, wanda a halin yanzu aka dakatar da shi a Najeriya, ya ce yana fatan za a ba shi damar ci gaba da harkokinsa bayan doguwar tattaunawa.

Bayanin na sa ya biyo bayan sanarwar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi cewa za a dage haramcin da aka yi wa kamfanin na tsawon watanni, amma sai bayan an cika wasu sharudda.Wani mai magana da yawun Twitter wanda ba a bayyana sunansa ba ya fitar da wata sanarwa ranar Juma’a, yana cewa ”Muna ci gaba da hulda da gwamnatin Najeriya kuma mun himmatu wajen tsara hanyar ci gaba don dawo da Twitter ga kowa a Najeriya.”

Ya kara da cewa ”Tattaunawa ce mai muhimmanci da fa’ida – muna fatan ganin an maido da aikin shafin nan ba da jimawa ba. “

Asalin hoton, TWITTER

Bayanan hoto,
Shugaban kamfanin Twitter Jack Dorsey

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za a iya dage takunkumin da aka sanya wa Twitter, amma sai idan kamfanin fasahar ya cika wasu sharudda.

Amma dokar ta ci gaba da aiki a safiyar Juma’a, duk da cewa Shugaba Buhari ya ce ‘yan Najeriya za su iya ci gaba da amfani da dandalin don “kasuwanci da abubuwan da ba su saba wa doka ba”.

A jawabin da ya yi na bikin ranar samun ‘yancin kan Najeriya, shugaban ya ce kwamitin shugaban kasa ya yi aiki tare da Twitter kan batutuwa da dama kama daga kan tsaron kasa, zuwa biyan haraji mai inganci da warware takaddama.

Gwamnatin Najeriya dai ta dakatar da ayyukan Twitter a watan Yuni, bayan da dandalin sada zumuntar ya goge wani sakon Twitter da ake ta ce-ce -ku -ce da cewa Shugaba Buhari ya yi wanda ya saba dokokinta.

Sakon ya yi magana game da yakin basasar Najeriya na 1967-1970.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...