Turkiyya na ƙoƙarin gano yadda aka kashe da kuma waɗanda ke da hannu a kisan Khashoggi

Lokacin da Khashoggi ke shiga ofishin jakadancin Saudiyya dake Santambul

Wata kotu a Turkiyya na ci gaba da shari’ar mutanen da ake zargi da kisan ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi, da aka kashe a ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Santambul a Turkiyya.

An kashe Mista Khashoggi wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman a shekarar 2018, abin da ya janyo martani daga ƙasashen duniya daban-daban.

Wani rahoton jami’ar bincike a kan kisan gilla ta majalisar ɗinkin duniya ya daddale cewa da hannun yarima mai jiran gado na Saudiyya a kisan Khashoggi, sai dai hukumomin Saduiia sun musanta zargin da suka kira a matsayin ƙanzon kurege.

Turkiyya da aka gudanar da kisan a cikinta, ta lashi takobin bankado masu hannu a kisan tare da ladabtar da su.

Saboda haka ne ma ta fara shari’a a kan wasu mutane 20 ƴan ƙsar ta Saudiyya da take zargi da hannu a kisan ɗn jaridar, sai dai ana shari’ar ne ba tare da mutanen da ake zargi ba.

Me Turkiyya ke son cimmawa dangane da shari’ar ?

Duk da cewa ba lallai ne shari’ar ta yi wani tasiri ba, wasu masu sharhi na da ra’ayin cewa ko ba komai za ta fito da ainihin abin da ya faru fili.

Ibrahim Shehu Adamu, wani ɗan jarida ne da ya yi zauna a Turkiyya, ya shaidawa BBC cewa abin da Turkiyya ke son yi shine nunawa duniya cewa da hannun hukumomin jagororin Saudiyya a kisan ɗan jaridar.

”Shari’ar ba ta da tasiri, amma a siyasance tana da matuƙar tasiri, Turkiyya na yi ne domin bayyanawa duniya waɗanda ke da hannu a kisan Khashoggi, musamman yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman”.

Ya ce babu wani hukunci da Turkiyya za ta iya dauka a kan mutanen ko da kotu ta same su da laifi, kasancewar ba ƴan kasarta bane, sannan ba a can suke zaune ba.

Su dai iyalan Jamal Khashogi sun ce sun yafewa wadanda suka kashe marigayin, abin da ke nufin cewa ita ma ƙasar za ta iya yafe musu a hukumance, in ji Ibrahim Shehu Adamu.

Bayanan bidiyo,
Hatice Cengiz, wadda Jamal Kashoggi za ya aura

A ranar Talata ne aka ci gaba da shari’ar da ake yi wa mutanen, tare da ƙara sunan mutum guda kan waɗnda ake zargi tun da farko.

A yayin zaman kotun wani abokin marigayin ɗan ƙsar Masar Ayman Noor ya shaidawa kotun cewa makusantan yariman mai jjiran gado na Saudiyya sun sha yi wa abokinsa barazana matsawar bai sanyawa bakinsa linzami ba.

More News

An hana fasinjoji hawa jirgi da jakar Ghana Must Go

Hukumar dake lura da filayen jiragen sama ta Najeriya FAAN ta sanar da matafiya ta filayen jiragen sama cewa daga yanzu ta haramta amfani...

Ƴan bindiga sun kai hari gidan kwamishinan zaɓe na jihar Kogi

Wasu yan bindiga sun kai hari gidan kwamishinan zaɓe na jihar Kogi dake Lokoja da tsakar daren ranar Alhamis. A cikin wata sanarwa da hukumar...

Gwamnan Kebbi ya sasanta wani rikicin manoma da makiyaya

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya sasanta rikicin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Suru da Koke Besse na jihar domin kawo zaman...

An sake gano gawar wani shugaban Fulani da ya ɓata a jihar Filato

An gano gawar wani Arɗon Fulani, Umar Ibrahim da ya ɓace a cikin wata rijiya dake kauyen Jokom a ƙaramar hukumar Mangu ta...