Tura ta fara kai wa bango, inji Bulama Bukarti

Katsina

Wani masanin harkokin tsaro dan Najeriya da ke Burtaniya Barista Bulama Bukarti ya bayyana fargabar ruruwar rikice-rikice a yankin arewacin Najeriya matukar gwamnatin kasar ta gaza yin daukar matakan da suka dace na dakile hare-haren.

A baya-bayan nan ne mazauna kauyen ‘Yantumaki da ke jihar Katsina a arewacin Najeriyar suka gudanar da zanga-zanga kan tabarbarewar tsaron da yankin ke fama da shi musamman yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da kazanta a yankin, lamari da ya yi asarar rayukan jama’a da dukiya mai yawa.

Barista Bukarti, ya ce hari na baya-bayan nan da aka kai a jihar Katsina – mahaifar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ce wanda a cewarsa alama ce ta nuna cewa “mutane sun gaji, sun kai iya wuya da rashin dakatar da kisansu da ake da kwace dukiyoyinsu da gwamnati ta kasa yi.”

Masanin ya ce lamarin izina ce ga gwamnatin don ta yi abin da ya kamata wajen samar da maslaha ga irin tashin hankalin da mutane ke fuskanta.

A cewarsa, zai yi wuya jama’a su dauki doka a hannunsu saboda an kwatanta irin haka a wasu jihohin ” Amma abin bai haifar da da mai ido ba, su wadannan marika makamai da ke arewa maso yammacin Najeriya suna da manya-manyan makamai kuma ba su da imani kwata-kwata,”

Ya ce, “Kuma al’ummar gari a ka’idar doka ba za su dauki bindiga ko makami su rike ba”. Ya bayyana cewa matukar gwamnati ba ta tashi tsaye ba, za a ci gaba da ganin irin wannan zanga-zanga kuma za ta ci gaba da kazanta kuma za ta ci gaba da ganin bore,”

“Kuma wannan ko ba komai sai ya jawowa ita jam’iyyar da take mulki faduwa a zabe na gaba, domin babu yadda za a yi ka yi mulki shekara hudu ko shekara takwas a yi ta kashe mutane kamar kiyashi, ka yi ta alkawari cewa za ka magance abin kuma ka kasa, kuma ka dauka cewa za a zabe ka a zabe na gaba.”

Barista Bukarti ya kuma ba da shawara kan matakan da ya kamata gwamnatin Najeriya ta dauka domin shawo kan matsalar tsaron da taki ci taki cinyewa:

Ayyana dokar ta baci

Masanin ya ce ayyana dokar ta bacin yana da matukar amfani saboda zai tabbatar da cewa an kai isassun sojoji da makamai sannan “kudaden ma da ba a sa su a cikin kasafin kudi a kan cewa za a kai wannan bangare ba (tsaro) shugaban kasa zai iya amfani da wannan dama, ya diba daga baitul mali don a je a yi yakin nan wato a gama da su wadannan ‘yan ta’adda”.

Ya ce ko a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ma an dauki irin wannan mataki kan Boko Haram lokacin da hare-harensu ya kazanta.

Gudanar da taron masu ruwa da tsaki

A cewar Barista Bulama, kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta jagoranci taron gwamnonin yankin arewa maso yammacin kasar da kuma masu fada aji na wannan yankin domin bayyana abubuwan da suka sa matsalar tsaron taki ci taki cinyewa.

Ya kara da cewa gudanar da taron zai ba da damar daukar matakai na gaske wanda “idan aka dauke su za a magance matsalar ta kare.”

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...