Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Obadia Mailafia Ya Mutu

VOA Hausa

Rahotanni daga Najeriya na cewa tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Dr. Obadia Mailafia ya mutu. Shekarunsa 64.

Kafafen yada labaran Najeriya da dama sun ruwaito cewa marigayin ya rasu ne a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a tsakar daren ranar Asabar.

Marigayin ya rike mukamin mataimakin babban bankin na Najeriya a tsakanin 2005 zuwa 2007. Sannan ya taba aiki a bankin raya kasashen Afirka na AFDB.

Bayan barin aikin gwamnati, Mailafia ya shiga harkokin siyasa, inda har ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC)

Ya kuma kasance mai yin fashin baki da rubuce-rubuce ga kafafen yada labarai kan al’amuran yau da kullum musamma a fannin tattalin arzikin Najeriya.

Ya yi karatun digirinsa a Jami’ar Ahmadu Bello Zari a (ABU,) inda ya kammala a shekarar 1978. Shi ne ya zo na daya a ajinsu a lokacin.

Marigayin ya kasance daya daga cikin masu fitowa su soki lamirin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan yadda take tafiyar da al’amuranta musamman kan abin da ya shafi harkar tsaro.

A bara, marigayin ya taba bayyana cewa wani gwamnan arewacin Najeriya ne kwamandan kungiyar Boko Haram, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce har hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyace shi ofishinta da ke Jos.

Sai dai a lokacin da yake amsa tambayoyi, Mailafia ya fadawa jami’an DSS cewa, ba shi da wata hujja ko shaida da za ta tabbatar da zargin da ya yi kamar yadda rahotanni suka nuna.

An haifi Mailafia a kauyen Randa da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna a arewa maso yanmacin Najeriya.

More News

An Kuɓutar Da Yara Arewa Da Aka Sayar A Kudancin Najeriya 

Cin zarafin da ake yi wa mutane na daga cikin matsalolin da ke ci gaba da dabaibaye Najeriya duk da fafutukar da hukumomi da...

”Yan bindiga sun kashe mutum 220 a Jihar Neja a watan Janairu kaɗai’

Gwamnan Jihar Neja a arewacin Najeriya ya ce 'yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 220 a jiharsa cikin wannan watan na Janairu kaɗai a...

Yadda ‘Yan bindiga Suka Tashi Wasu Garuruwa Tara A Jihar Kaduna

Sai dai hukumomin tsaro na ikirarin cewa suna samun nasara akan 'yan fashin dajin a hare-haren da suke kai musu. A daidai lokachin da...

An bai wa gwamnatin Buhari shawarar kara farashin fetur zuwa N302

Watakila gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai zuwa, Fabrairu, kamar yadda majalisar...