Tony Blair, tsohon Firayim Ministan Burtaniya, ya ziyarci Asiwaju Bola Tinubu, shugaban kasa mai jiran gado, a ranar Talata.
Wannan dai na zuwa ne mako guda kafin rantsar da zababben shugaban kasar.
Wata majiya ta kusa da zababben shugaban kasar ta tabbatar da ziyarar ta Blair, inda ta kara da cewa ya kai ziyarar ne domin tattaunawa da Mista Tinubu.
Ya ce, “Bani da cikakken bayani tukuna. Amma na yi imanin hakan na da nasaba da kulla alaka tsakanin Najeriya da Birtaniya. Ina fata kuna sane da cewa Sakataren Amurka ma ya kira Asiwaju a makon jiya.”
Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da mataimakin shugaban kasa mai jiran gado Kashim Shettima sun halarci taron.
