Ministan ayyuka, David Umahi ya gayyaci masu kamfanonin siminti kan yadda farashin siminti ke cigaba da ƙaruwa a kasuwanni.
A yanzu dai farashin siminti na yawo ne daga kan ₦8000 zuwa ₦10000 ba kamar ₦4000 ba da aka riƙa sayar da shi makonni biyu da suka wuce.
Kamfanonin Dangote, BUA da kuma Lafarge na daga cikin kamfanonin siminti da ma’aikatar ayyukan ta gayyata domin ganawar da su.
Orji Uchenna Orji mai taimakawa ministan kan harkokin ƴada labarai ya ce yadda ake amfani da siminti da yawa sosai kama daga yin tituna da gidaje ya sa ministan ya damu da ƙaruwar farashin.
Ministan ayyukan ya ce banbancin dake tsakanin kuɗin siminti a farashin kamfani da kuma yadda ake sayarwa a waje yana da yawa sosai.