Tinubu Zai Yi Idin Ƙaramar Sallah A Lagos

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu zai bar Abuja zuwa Lagos ranar Lahadi gabanin bikin ƙaramar sallah.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya ce Tinubu zai yi amfani da lokacin tare da iyalinsa  wajen yiwa Najeriya addu’a.

Ngelale ya ce shugaban ƙasar zai cigaba da gudanar da ayyukansa daga Lagos a lokaci da kuma bayan hutun sallah.

A ranar Litinin ne za a fara duban watan Shawwal b bayan da watan Azumin Ramadan ya cika kwanaki 29.

More from this stream

Recomended