Tinubu zai rantsar da sababbin ministoci ranar Litinin

Shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu zai rantsar da sababbin ministoci a ranar Litinin bayan da majalisar dattawa ta tabbatar da su.

Mashawarci na musamman ga shugaban ƙasar kan kafafen yaɗa labarai, Bayo Onanuga shi ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Bikin rantsar da ministocin zai gudana ne a dakin taro na majalisar zartarwa ta tarayya dake fadar shugaban ƙasa.

A ranar 25 ga watan Oktoba ne shugaban ƙasar ya sanar da korar ministoci 5 daga gwamnatinsa inda ya naɗa wasu 7 tare da sauyawa wasu 10 ma’aikatu.

Ministocin da za a rantsar sun haɗa da Nentawe Yilwatda, Muhammad Maigari Dingyaɗi, Suwaiba Sa’idu Ahmad, Bianca Odumegwu Ojukwu, Yusuf Abdullahi Ata, Muktar  Idi Maiha da kuma Jumoke Oduwale

More from this stream

Recomended