Tinubu ya umarci kamfanonin siminti su koma sayarwa a tsohon farashi

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya umarci kamfanonin da suke samar da siminti da su cigaba da sayar da simintin akan farashin da suke sayarwa a baya.

Ministan Ayyuka, David Umahi shi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan da ya kammala zagayawa kamfanin siminti na BUA dake Sokoto.

A cewar ministan  a lokacin ganawar da aka yi da kamfanonin simintin, shugaban ƙasar ya umarce su da su koma sayarwa akan tsohon farashin.

Umahi ya yabawa kamfanin na BUA kan yadda suka kammala aikin gina wurin sarrafa siminti na biyar dake kamfanin.

A yayin ziyarar ministan na tare da shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

More from this stream

Recomended