Tinubu Ya Tafi Tanzania Domin Halartar Taro A Kan  Makamashi

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi Tanzania a ranar Lahadi domin halartar taron ƙoli na Afirka kan makamashi da za a gudanar a Dar es Salaam, babban birnin ƙasar. Taron zai fara yau Litinin kuma ya ƙare gobe Talata.

Taron na musamman wanda gwamnatin Tanzania za ta karɓi baƙuncinsa tare da haɗin gwiwar Bankin Raya Afirka da Bankin Duniya, yana da nufin tabbatar da samar da wutar lantarki ga mutum miliyan 300 a Afirka nan da shekara ta 2030, karkashin shirin da aka sanya wa suna ‘‘Mission 300.’’

A wannan taron, shugabannin kasashen Afirka, masana harkokin kasuwanci, da kungiyoyin farar hula za su tattauna kan dabarun da za su taimaka wajen cimma wannan babban buri cikin gaggawa.

Bugu da ƙari, taron zai kuma mayar da hankali kan musayar dabaru da hanyoyin da za a bi don magance matsalar makamashi a nahiyar Afirka.

More from this stream

Recomended