Tinubu ya naɗa sabbin majalisun gudanarwar jami’o’i a Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin wasu mutane a majalisar gudanarwar jami’o’in gwamnatin tarayya da manyan makarantun ilimi.

A wata sanarwa da kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Laraba, shugaban ya nada Temi Harriman, shugaba;  Adeola Adeogun, Benedict Aguele, Freeman Kasa, Babangida Abdullahi, a matsayin memba na Hukumar Jami’ar Maritime ta Najeriya, Okerenkoko, Delta.

Shugaban ya kuma nada Rabe Mudi Bala shugaban hukumar Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Najeriya, Abuja; Akinola Fagbemi, Rakiatou Bagnou, Alwel Egwurugu da Femi Osabinu, a matsayin mambobi a Majalisar.

Sauran nadin dai sun hada da: Bram Baifa a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin jami’ar noma ta tarayya Bassam-Biri Bayelsa, tare da Richard Odigbo, Yomi Johnson, Fatima Owuna da Christy Omoruyi a matsayin mambobi.

More from this stream

Recomended