Tinubu Ya Dawo Najeriya Daga Qatar

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauka a Abuja babban birnin ƙasarnan bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai ƙasar Qatar.

Tinubu ya sauka a Abuja da maraicen ranar Litinin inda ya samu tarba daga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

More from this stream

Recomended